Littafin IBB Ya Tono Tsuliyar Dodo, An Fadi Kabilar da Ake So Ta Yi Mulki a 2027

Littafin IBB Ya Tono Tsuliyar Dodo, An Fadi Kabilar da Ake So Ta Yi Mulki a 2027

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Charles Udeogaranya, ya ce littafin Janar Ibrahim Babangida ya fito da bukatar bai wa Ibo mulki
  • A cikin littafin, IBB ya bayyana cewa ba Ibo ne kaɗai suka shirya juyin mulkin 1966 ba, yana mai fito da manufar da ta sa aka yi juyin
  • Udeogaranya ya bukaci jam'iyyun APC, PDP da LP su tsayar da ‘yan takara daga Kudu maso Gabas, yana mai cewa hakan zai kawo adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Charles Udeogaranya, ya ce bayanan Janar Ibrahim Babangida za su share hanyar ba Ibo damar yin mulki a 2027.

Udeogaranya ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, yayin da ake ci gaba da kiran a bai wa kabilar Ibo damar yin shugabanci.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Peter Obi ya hango rugujewar LP, ya fadi makomarsa a 2027

Tsohon dan takarar APC ya nemi a ba dan Ibo takarar shugabancin Najeriya a 2027
Tsohon jigon APC na so a zabi dan Ibo a matsayin shugaban kasa a 2027. Hoto: NGRPresident
Asali: Twitter

Bayanin IBB kan juyin mulkin 1966

Maganganun nasa na zuwa ne bayan Babangida a littafinsa ya bayyana cewa ba Ibo ne kadai suka shirya juyin mulkin 1966 kaɗai ba, inji rahoton Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Babangida, ba a aiwatar da juyin mulkin 1966 bisa ƙabilanci ba, sai dai don sake fasalin tsarin mulkin Najeriya, akasin abin da ake yawan zato.

Ya kuma jaddada cewa Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, wanda aka fi dangantawa da juyin mulkin, yana da cikakkiyar fahimtar ƙasa baki ɗaya.

Juyin mulkin 1966 ya haifar da mutuwar fitattun ‘yan siyasa daga Arewa da Yamma, lamarin da ya bar babban tabo a tarihin Najeriya.

Mafi yawan wadanda suka jagoranci hambarar da gwamnatin 'yan kabilar Ibo ne, sai dai IBB ya ce Kaduna Nzeogwu yana Hausa radau.

Ana so Ibo su yi mulkin Najeriya a 2027

Rahoton ya ce wasu sun yi amfani da wannan lamari wajen ganin an hana yankin Kudu maso Gabas takarar shugabancin ƙasa na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya fallasa yan siyasa da suka ba shi cin hancin N500m

Bayan fitar da littafin rayuwar IBB, kungiyoyin Ibo irin su Ohanaeze Ndigbo sun nuna bukatar a ba su hakuri kan wariyar da suka fuskanta a siyasance na tsawon lokaci.

Charles Udeogaranya ya ce bayanin Babangida ya wanke mutanen Ibo daga duk wani zargi, sannan ya buɗe hanya ga fitowar shugaban ƙasa daga yankin a 2027.

Ya ce idan har ana so ayi adalci kuma a nuna haɗin kan ƙasa, to akwai bukatar a miƙa mulki ga Kudu maso Gabas a zaben 2027.

“An ƙirƙiri waɗannan ƙaryace-ƙaryacen don hana ‘yan Ibo mulki tsawon shekaru, amma lokaci ya yi da za a gyara kura-kuran da aka yi,” inji Udeogaranya.

"APC, PDP, LP su ba Ibo takara" - Udeogaranya

Charles Udeogaranya ya nemi jam'iyyun siyasa su ba dan kabilar Ibo tikitin takara
Charles Udeogaranya, tsohon mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.
Asali: UGC

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci manyan jam’iyyu, irinsu APC, PDP da LP da su tsayar da ‘yan takara daga Kudu maso Gabas a 2027.

Kara karanta wannan

Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana zai maka Janar Babangida a kotu, ya jero dalilai

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen warkar da ƙasar nan da dawo da ita kan hanyar bunƙasa ta fuskar tattalin arziki da ci gaba.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo dai ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya bayar da hakuri da kuma biyan diyyar Naira tiriliyan 10 ga mutanen Ibo.

Kungiyar ta ce bayanin Babangida ya nuna buƙatar a shawo kan ƙorafe-ƙorafen da suka shafi tarihin siyasar Najeriya na tsawon lokaci.

Atiku, Obasanjo sun je kaddamar da littafin IBB

A wani labarin, mun ruwaito cewa, manyan shugabannin Najeriya, ciki har da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, sun hallarci kaddamar da littafin rayuwar IBB.

An shirya kaddamar da littafin mai suna 'A Journey in Service' a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu, a nan Ibrahim Babangida ya tona badakalar 12 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.