Duka Shugabannin Najeriya Da Suka Mutu Daga 1966 Kan Mulki Da Yadda Ajalinsu Ya Kasance

Duka Shugabannin Najeriya Da Suka Mutu Daga 1966 Kan Mulki Da Yadda Ajalinsu Ya Kasance

A tarihin Najeriya, an yi shugabannin soja da na farar hula 15. Wasu daga cikinsu, sun mutu ne yayin da su ke ofis, kafin su kammala wa’adinsu.

A yau kuma, Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin wadannan shugabanni da ajali ya riske su a ofis.

Daga cikinsu akwai wadanda aka yi wa kisan gilla, sannan akwai wadanda rashin lafiya ta kashe su. Wani kuma har yanzu ba a san gaskiyar ajalinsa ba.

1. Abubakar Tafawa-Balewa

Shugaban farko da aka kashe shi ne Firayim Ministan farko (kuma na karshe), Abubakar Tafawa-Balewa. Sai bayan kwanaki aka ga gawar Firayim Ministan a jeji.

An hallaka Tafawa-Balewa ne a juyin-mulkin da aka yi na ranar 15 ga watan Junairun shekarar 1966, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugabannin farko na kasa.

KU KARANTA: Dalilin Sojoji na kashe zaben MKO Abiola a 1993 - Obasanjo

Kara karanta wannan

Sata a CBN: Gwamnati ta roki INTERPOL a kama mutum 3 da suka yi amfani da sa hannun Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Jonathan Thomas Aguiyi Ironsi

Watanni shida da hallaka Abubakar Tafawa-Balewa a 1966, sai wasu sojoji suka sake yin juyin-mulki, suka hambarar da gwamnatin Janar JTU Aguiyi Ironsi a Yuni.

Kamar yadda aka kashe Firayim Minista da wasu a baya, Aguiyi Ironsi wanda shi ne shugaban soja na farko da aka yi, ya gamu da mummunar kisan gilla a Ibadan.

3. Murtala Mohammed

A Fubrairun 1976 ne Kanal S. B Dimka da wasu mutanensa su ka nemi su hambarar da gwamnati, har su ka yi nasarar kashe Janar Murtala Mohammed da tsakar safiya.

Sojojin tawayen sun buda wa motar Janar Murtala Mohammed wuta a hanyarsa ta zuwa ofis. A karshe an kama wadanda su ka yi wannan danyen aiki, aka kashe su.

Duka shugabannin Najeriya da su ka mutu daga 1966 a kan mulki da yadda ajalinsu ya kasance
Ummaru Musa Yaradua Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Abubuwa da ya kamata ka sani game da 'Yaradua

4. Sani Abacha

Kara karanta wannan

Yadda Sarkin Kano Aminu Bayero Ya Saba da Sanusi II a Kan Maganar Dauke Ofisoshin CBN

A 1998 ne Shugaba Janar Sani Abacha ya mutu a wani irin yanayi da har yanzu ba a gama gane abin da ya faru ba. Abacha ya mutu ne a gadonsa a fadar shugaban kasa.

Sani Abacha wanda ya yi juyin mulki na karshe a Najeriya ya rasu bayan ya yi shekaru biyar ya na mulki, har an fara shirin ya cire kayan soja, ya shiga zaben farar hula.

5. Ummaru Musa ‘Yar’adua

Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua ya rasu a Mayun 2010 ya na da shekaru kusan 60. Shugaban kasar ya yi ta fama da larurar rashin lafiya wanda a karshe ta zama ajalinsa.

Ana tunanin Ummaru Musa ‘Yaradua ya mutu ne a sakamakon matsalar ciwon zuciya, hunhu da koda da ya yi ta fama da su tun tuni, shi ne shugaba na karshe da ya rasu a ofis.

A jiya kun ji abin da mutane ke fada game da Shugaba Ummaru ‘Yar’adua a dandalin Twitter shekaru 11 da rasuwarsa. Mutane sun ce an yi rashin tsohon Shugaban Najeriyar.

Kara karanta wannan

AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe

Wani Bawan Allah ya ce: ‘Yaradua ne shugaban kasa na karshe da aka yi, yanzu gararamba ake yi. Shi kuma wani ya tuna yadda tsohon Shugaban kasar ya rage farashin fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng