Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban NYSC Ana tsaka da Dambarwar Biyan ₦77,000

Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban NYSC Ana tsaka da Dambarwar Biyan ₦77,000

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta Janar na NYSC
  • Kafin nada shi ya kasance daga cikin manyan jami'an Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da masu bautar kasa ke bukatar biyan sabon mafi karancin albashi na ₦77,000 a wata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Birgediya Janar Nafiu ya karbi ragamar shugabancin NYSC ne daga hannun tsohon Darakta-Janar, Birgediya Janar Yushau Ahmed.

Shugaban NYSC
Tinubu ya nada sabon shugaban NYSC. Hoto: NYSC Jigawa State|Zagazola Makama
Source: Facebook

Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa Birgediya Janar Nafiu ya rike mukamai daban daban a rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata

Nadin Birgediya Janar Nafiu na zuwa ne a daidai lokacin da masu bautar kasa ke ci gaba da kiran gwamnatin tarayya da ta biya su sabon mafi karancin albashi na ₦77,000 maimakon ₦33,000.

Bola Tinubu ya nada sabon shugaban NYSC

Sabon shugaban NYSC da Bola Tinubu ya nada, Birgediya Janar Kunle Nafiu ya fito ne daga Ileogbo, karamar hukumar Aiyedire ta jihar Osun.

Kafin nadinsa, ya kasance Shugaban Ma’aikatan Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanal Janar Janar Olufemi Oluyede.

Vanguard ta wallafa cewa Birgediya Janar Nafiu kwararren jami’i ne da ya kammala karatu a makarantar sojoji kuma ya yi karatu a makarantar soji a kasar Amurka.

Haka kuma, ya taba zama Malami mai koyarwa a wata makarantar soji da ke Najeriya kafin daga bisani a nada shi Shugaban Ma’aikatan Hafsan Sojojin Kasar.

Kalubalen sabon shugaban NYSC

Nadin Birgediya Janar Nafiu na zuwa ne a daidai lokacin da masu bautar kasa ke korafi kan rashin biyan su sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun taru sun ba shugaba Bola Tinubu mukamin sarauta mafi girma

Tun bayan da gwamnati ta bayyana sabon mafi karancin albashi na ₦70,000, masu bautar kasa na ci gaba da kokawa kan yadda ake ci gaba da biyansu ₦33,000.

Masu bautar kasar suna sa ran cewa sabon Darakta-Janar din zai mayar da hankali wajen ganin an kara musu kudin din da ake basu a wata.

NYSC N
Tsohon shugaban NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed. Hoto: National Youth Service Corps
Source: Facebook

Wani da ke bautar kasa a Abuja ya bayyana wa Legit cewa:

“Muna fatan sabon shugaban NYSC zai kawo mafita ga batun albashinmu, saboda da yawa daga cikin mu suna fama da matsalar kudi.”

Masana na ganin cewa ya kamata sabon Darakta-Janar ya duba yadda za a tabbatar da ingantaccen tsarin kula da masu bautar kasa.

Haka zalika sun ce akwai bukatar a samar da karin hanyoyin saukaka wa masu bautar kasa rayuwa, musamman ta fuskar jin dadin su da kuma walwala yayin gudanar da hidimar kasa.

Ana sa ran cewa jagorancinsa zai taimaka wajen tattaunawa da hukumomin da suka dace don ganin an aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashi ga masu bautar kasa.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

An sace tsohon shugaban hukumar NYSC

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun hada gangami sun sace tsohon shugaban NYSC, Manjo Janar Maharazu Ibrahim Tsiga mai ritaya.

Rahotanni sun nuna cewa an sace tsohon shugaban ne a gidansa a jihar Katsina kuma bayan shafe kwanaki a hannun 'yan bindiga, har yanzu ba a ceto shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng