Daga Fara Ramadan, Ana Barazanar Rufe Najeriya Kirif da Zanga Zanga ga Tinubu

Daga Fara Ramadan, Ana Barazanar Rufe Najeriya Kirif da Zanga Zanga ga Tinubu

  • Kungiyar NLC ta gargadi mambobinta da su shirya yajin aiki a dalilin karin kudin wutar lantarki da na sadarwa
  • NLC ta ce ba za ta lamunci rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya ba tsakaninta da gwamnatin tarayya ba
  • Kungiyar ta zargi NERC da kokarin tauye hakkin 'yan Najeriya ta hanyar tursasa musu karin kudin shan wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Kungiyar Kwadagon Najeriya (NLC) ta bayyana rashin jin dadinta kan karin kudin hidimar sadarwa da kuma shirin karin kudin wutar lantarki da ake kokarin aiwatarwa.

Shugabannin kungiyar sun yi wannan furuci ne yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ta gudanar a Yola, jihar Adamawa.

NLC Najeriya
'Yan gwadago na shirin zanga zanga kan karin kudin wuta. Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Labour Congress HQ
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta NLC ta bukaci mambobinta da su kasance cikin shirin tsaf domin gudanar da yajin aiki matukar gwamnati ta zartar da karin kudin wuta.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun taru sun ba shugaba Bola Tinubu mukamin sarauta mafi girma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika 'yan kwadago sun ce za su yi zazzafan zanga zanga a kan karin kudin wutar da gwamnati ke shirin yi.

Yarjejeniyar NLC da gwamnatin tarayya

Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, da Sakatare Janar, Emmanuel Ugboaja, sun ce har yanzu suna kokwanto kan aniyar gwamnati na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.

'Yan kwadago sun bayyana cewa a ranar 21 ga Fabrairu, 2025 suka cimma yarjejeniyar da gwamnatin tarayya.

Sun bayyana cewa sun kulla yarjejeniyar ne don rage yawan karin kudin sadarwa daga kaso 50% zuwa kaso 35%.

A karkashin haka NLC ta ce idan har ba a aiwatar da hakan ba kamar yadda aka amince, za su dauki matakin da ya dace.

Zargin tauye hakkin jama'a a Najeriya

Kungiyar NLC ta bayyana matakin hukumar NERC na sake rarraba masu amfani da lantarki bisa la’akari da ingancin hidima a matsayin wata dabara ta kara kudin wuta ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Bashi: Obasanjo da tsofaffin shugabannin kasashe 7 sun roka wa Afrika yafiya

A cewar kungiyar, sabon tsarin zai jefa 'yan kasa cikin halin kaka-ni-ka-yi ta hanyar mayar da su zuwa sahun Band A, wanda zai tilasta musu biyan kudin wuta mai tsada.

Kungiyar ta ce hakan bai dace ba lura da halin da 'yan kasa ke ciki na rugujewar tattalin arziki da matsin rayuwa.

Shirin yajin aiki da zanga zanga a Najeriya

NLC ta gargadi cewa idan har gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma za ta dauki matakin yajin aiki da zai jawo rufe Najeriya kirif da tsayar da lamura cak.

Jaridar Punch ta wallafa cewa NLC ta ce za ta yi zanga zanga a dukkan fadin Najeriya idan har aka aiwatar da karin kudin wutar.

Kungiyar ta bukaci dukkan mambobinta da sauran ‘yan kasa da su kasance cikin shiri domin fuskantar duk wani mataki na rashin adalci da gwamnati za ta dauka.

Zanga zanga
Matasan Najeriya yayin wata zanga zanga. Hoto: Kola Sulaimon
Source: Facebook

Kudin wuta: Kungiyoyi za su yi zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyi masu zaman kansu sun yi barazanar fara zanga zanga a fadin Najeriya kan karin kudin wuta.

Kungiyoyi da 'yan kasuwa sun ce karin kudin wuta da gwamnati ke shirin yi zai iya kawo koma-baya a harkokin kasuwanci a kashe sana'o'i.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng