Ana Binciken Natasha maimakon Akpabio duk da Zargin Shugaban Majalisa da Lalata

Ana Binciken Natasha maimakon Akpabio duk da Zargin Shugaban Majalisa da Lalata

  • A karon farko, majalisar dattawan kasar nan ta magantu a kan dambarwar dake tsakanin shugabanta, Godswill Akpabio da Sanata Akpoti-Uduaghan
  • Jami'in hulda da jama'a na majalisar, Yemi Adaramodu ne ya yi magana a yammacin Lahadi, inda ya ce su na jin batun ne kafafen yada labarai
  • Ya ce ita kuma majalisa ba ta daukar batun dake yawo a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta, saboda haka babu abin da za ta yi a kai
  • Yayin da majalisar ke shirin binciken Natasha, ya kara da cewa za a iya daukar mataki a kan batun matukar aka cika sharadin da ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMajalisar Dattawa ta bayyana cewa ba za ta binciki zargin neman Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ba. Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha, ta yi zargin cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya nemi ya yi lalata da ita, kuma kin amince masa ya jawo mata matsala a majalisa.

Kara karanta wannan

Akpabio: An tono yadda Natasha ta taba zargin Omokri da nemanta da lalata a 2014

Majalisa
Majalisa ta fadi matsayarta a kan zargin Natasha Hoto: Hoto: The Nigeria Senate
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito kakakin Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu, ya ce a halin yanzu, babu wata takardar korafi da aka gabatar a gaban majalisa kan batun cin zarafin. Ya kara da cewa saboda haka, majalisar ba za ta tsoma kanta a cikin batun ba, amma akwai bincike da za ta yi a kan 'yar majalisar.

Majalisa za ta binciki Natasha

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Yemi Adaramodu ya ce abin da majalisa ta sa a gaba na bincike a yanzu, shi ne zargin karya dokokin majalisa da Sanata Natasha ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha
Majalisa za ta binciki Natasha bisa zargin karya doka Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Ya ce:

“Babu wata tuhuma da ke gaban Majalisar Dattawa. Babu daga kowa ko daga kowace hukuma. Don haka ba ma daukar tuhumomi daga talabijin ko kafofin sada zumunta. Babu wanda ya kai wani korafi ga majalisa ko wani bangare na majalisar.
“Saboda haka, batun da ke gaban majalisa kawai shi ne karya dokokin majalisa, wanda aka tura zuwa kwamitin Majalisa kan ladabtarwa, dabi’u da korafe-korafe.”

Kara karanta wannan

Natasha: Atiku ya tsoma baki a zargin shugaban majalisa da neman lalata

Natasha: Babu wanda ya kai korafi ga majalisa

A cewar Adaramodu, har sai an gabatar da wani korafi na zargin cin zarafin Sanata Natasha a hukumance, sannan za a dauki mataki a kan batun yadda ya kamata.

Ya nanata cewa amma a halin yanzu, babu wata tuhuma da aka tura ga majalisa banda wadda ke gaban kwamitin. Ya ce:

“Kuma ban ga wata takardar korafi ko wata kara da ke gaban kwamitin ba. Muna iya jin abubuwa da dama daga waje, amma a cikin majalisa, babu wata tuhuma da ke kan kowa, babu wata kara daga kowa, kuma babu wata shari’a da aka gabatar a gabanmu."

Atiku: "A binciki zargin Natasha kan Akpabio"

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadin yadda ake samun batun zargin cin zarafi daga majalisar dattawan Najeriya.

Ya ce zargin cin zarafin mata a wurin aiki yana daga cikin abubuwan dake dakile ci gaban mata a kasar nan, saboda haka ya ce akwai bukatar a yi bincike mai zurfi a kan zargin Natasha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.