Sarkin Sasa: Awanni da Birne Shi, an Sanar da Sabon Basarake da Zai Maye Gurbinsa
- An birne Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin Katsina, wanda ya rasu yana da shekara 125, a gidansa da ke Sasa, Ibadan, Oyo a yau Lahadi.
- 'Ya'yansa da shugabannin Arewa a Kudu sun zabi ɗansa, Ahmed Haruna (Ciroma) a matsayin sabon Sarki don cike gibin da marigayin ya bari
- Gwamna Seyi Makinde da wasu sanatoci sun yi alhinin rasuwar Sarkin, suna yabawa da gudunmuwarsa, suna addu’ar Allah ya gafarta masa
- Hakan ya biyo bayan sanar da rasuwar Sarkin a jiya Asabar 1 ga watan Maris, 2025 wanda ya shafe shekaru kan karagar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Bayan sanar da labarin rasuwarsa, an binne gawar Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin Katsina.
Sarkin Sasa ya rasu yana da shekara 125 a duniya wanda aka binne a gidansa da ke unguwar Sasa, karamar hukumar Akinyele, Ibadan.

Kara karanta wannan
'Mun yi babban rashi': Gwamna ya girgiza da mutuwar sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin

Asali: Facebook
An nada sabon Sarkin Sasa a Oyo
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an binne marigayin da misalin karfe 1:45 na ranar yau Lahadi 2 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa a jihohi 17 na Kudancin Najeriya.
Domin kauce wa gibin shugabanci, iyalinsa da shugabannin Arewa a Kudu sun amince da nadin dansa, Ahmed Haruna (Ciroma), a matsayin sabon Sarki.
A wani taro da aka yi a yau Lahadi, an kafa kwamiti don sanar da Olubadan na Ibadan kafin bikin nadin sabon Sarkin a lokacin addu’ar makoki..
Yadda aka bi tsarin nada sabon Sarki
Wani na kusa da iyalan ya ce:
“Taron ya tattauna kan sabon Sarkin Sasa, dole a samu magaji, an cimma matsaya kuma Olubadan zai tabbatar da nadin.”
Shugaban Sarakunan Arewa, Suleiman Rabiu, ya tabbatar da nadin, yana cewa shugabanni daga jihohi 17 sun halarci jana’izar da taron nadin magajin.

Kara karanta wannan
Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan
Rabiu, wanda shi ne Sarkin Hausawan Lagos, ya kara da cewa:
“Mun nada Ciroma, daya daga cikin ‘ya’yan marigayi, dukkan ‘ya’yansa sun amince da hakan.”
“Tun farko mun gargade su da su mara wa sabon Sarki baya, bai kamata ya zama mai neman kudi da mukaminsa ba.”

Asali: Twitter
Sarkin Sasa: Gwamna ya tura sakon ta'azziya
Gwamna Seyi Makinde ya ce rasuwar Sarkin Sasa “karshen wani babi ne,” yana jajantawa iyalansa da al’ummar Hausa/Fulani na Oyo da Kudancin Najeriya.
A cikin wata sanarwa, ya ce:
“Na san marigayin tun kafin in zama gwamna, ya kasance mai goyon baya ga gwamnatina, Allah ya jikansa, mun yi aiki tare, Allah ya gafarta masa, ya sa Aljanna Firdausi makomarsa.”
Sanatocin APC daga Oyo ta Tsakiya da Oyo ta Kudu, Yunus Akintunde da Sharafadeen Alli, sun nuna alhininsu game da rasuwar Sarkin.
Rigimar sarauta: Gwamnatin Kano ta roki Tinubu

Kara karanta wannan
Ana murnar fara azumi, sanatan Arewa ya shirya gagarumin bikin tallafawa talakawa
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga Fadar Nasarawa.
Gwamnatin ta ce hakan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kowa ke bukata tun bayan rigimar sarauta.
Asali: Legit.ng