Masu Safarar Yara Sun Yiwa 'Yan Sandan Najeriya Tayin Cin Hancin Naira Miliyan 1
- Rundunar ‘yan sandan Imo ta cafke mutum biyu da ake zargi da safarar yara tare da ceto yara biyu da aka sace a wurare daban-daban
- Kakakin rundunar, Henry Okoye, ya ce jami’an sun nuna kwarewa wajen kin karbar cin hancin Naira miliyan daya domin tabbatar da adalci
- An ceto yaran da aka sace, kuma bincike ya nuna akwai babbar cibiyar safarar yara da ake kokarin bankadowa yanzu haka a jihar Imo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da safarar yara, tare da ceto yara biyu da aka sace a wurare daban-daban.
Kakakin rundunar, Henry Okoye, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun nuna kwarewa wajen kin karbar cin hancin Naira miliyan daya domin tabbatar da adalci.

Asali: Twitter
'Yan sanda sun ki karbar cin hancin N1m
Jaridar Vanguard ta rahoto Henry Okoye yana cewar, jami’an rundunar da ke gudanar da bincike a titin Owerri-Aba suka kama wata mata mai suna Eze Chika, mai shekaru 45.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okoye ya ce, a binciken 'yan sandan na ranar 21 ga Fabrairu, an samu matar da wani yaro dan shekara hudu da aka sato, amma a farko ta yi ikirarin cewa dan nata ne.
Daga baya, ta amsa cewa ta sayi yaron daga wajen wata kungiya da ake zargin ta masu safarar yara ce a garin Aba, a kan kudi Naira miliyan 1.8.
Da take kokarin tserewa daga hukunci, matar ta yi yunkurin ba wa jami’an ‘yan sanda cin hanci na Naira miliyan daya, amma suka ki karba.
Jami’an sun cafketa tare da ceto yaron cikin koshin lafiya, kuma bincike ya nuna tana da alaka da wata babbar cibiyar safarar yara.
An kama matar da ta sace yaron makociyarta
A wata sabuwar nasara, jami’an SCID sun kama wata mata mai suna Confidence Odo, mai shekaru 32, bisa zargin sace yaron tsohuwar makwabciyarta.

Asali: Twitter
Rahotanni sun bayyana cewa Odoh ta saci yaron ne a ranar 4 ga Fabrairu, yayin da yake wasa a harabar gidansu.
An ceto yaron kuma aka mayar da shi hannun iyayensa, Mista da Misis Michael Ududiri, yayin da ake ci gaba da farautar masu hannu a satar.
'Yan sanda sun ba da lambar tuntuba
Kakakin ‘yan sandan ya jaddada aniyar rundunar wajen yaki da safarar yara da sauran manyan laifuka a jihar Imo.
Ya bukaci iyaye su kasance masu lura da ‘ya’yansu tare da hana su yawo ba tare da wani sa ido ba.
Rundunar ta kuma bukaci al’umma su rika kai rahoton duk wani motsi da suke zargin na masu safarar yara ne zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Domin bayar da rahoto kai tsaye, rundunar 'yan sandan ta bayar da lambobin kira kamar haka: 08034773600 da 08148024755.
'Yan sanda sun ki karbar cin hancin N174m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen Legas sun bayyana cewa sun ki karbar cin hanci daga wani dan damfara, Patrick Akpoguma.
A cewar rundunar, wanda ake zargin, wanda ke damfarar mutane ta yanar gizo, ya yi kokarin ba su rashawa har Naira miliyan 174 domin kaucewa hukunci.
An ce Akpoguma ya shahara wajen yaudarar mutane ta hanyar soyayya, satar kudi, da tsafi ta yanar gizo, lamarin da ya sa yake kokarin kubuta daga hannun ‘yan sanda.
Asali: Legit.ng