Ramadan: Ganduje Ya Tuna da Musulman Najeriya, Ya ba da Shawara

Ramadan: Ganduje Ya Tuna da Musulman Najeriya, Ya ba da Shawara

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya al'ummar Musulmai murnar shigowar watan azumin Ramadan
  • Ganduje ya buƙaci al'ummar Musulmai da su kasance masu taimakon talakawa da mabuƙata da dagewa wajen yin ibada
  • Shugaban na APC ya kuma buƙaci ƴan Najeriya kan su ci gaba da addu'o'i ga mai girma Bola Ahmed Tinubu wajen sauke nauyin da ke kansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ƴan Najeriya kan azumin watan Ramadan.

Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci al’ummar Musulmi da su tuna da talakawa da mutane masu rauni yayin da suke gudanar da azumin watan Ramadan.

Ganduje ya ba musulmai shawara
Ganduje ya bukaci Musulmai su tuna da talakawa a Ramadan Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ganduje ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murnar shigowar Ramadan da babban sakataren yaɗa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya yi hangen nesa, ya gano hanyar magance rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya tura saƙo kan Ramadan

Shugaban na APC ya bayyana cewa lokacin watan azumin watan Ramadan lokaci ne na komawa ga Allah.

“Ramadan wata ne na zage damtse wajen ibada da kuma ƙarfafa imani, muna roƙon Allah (SWT) da Ya ba mu ƙwarin gwiwa da hikima don gudanar da azumi cikin jajircewa da gaskiya."
"Yayin da muka shiga wannan tafiya ta kwanaki 30, muna kira ga dukkan Musulmin Najeriya da su kasance masu riƙe imaninsu, tare da ci gaba da zama abin koyi wajen tausayi, kyauta, da jin ƙai, waɗanda su ne ginshiƙan addininmu."

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta walwala da jin daɗin kowa da kowa, ba tare da la’akari da addini ko asalin mutum ba.

"Za mu ci gaba da aiki tuƙuru don shawo kan ƙalubalen da ke fuskantar ƙasarmu, tun daga matsalar tattalin arziƙi har zuwa rashin daidaito a cikin al’umma."

Kara karanta wannan

"Kai matsoraci ne": Minista ya yi kaca kaca da mataimakin Abba kan sukar Tinubu

"Yayin da muke yin azumi, mu tuna da waɗanda suka fi buƙata a cikinmu, talakawa, masu rauni, da waɗanda aka ware."
"Mu taimake su cike da tausayi, kyauta, tare da yin aiki tare domin gina al’umma mai haɗin kai da adalci."

- Abdullahi Umar Ganduje

Wace shawara Ganduje ya ba da?

Har ila yau, ya buƙaci Musulmin Najeriya da su yi addu’a ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin Allah Ya ba shi iko da hikima wajen aiwatar da manufofinsa wanda ke da nufin kawo ci gaba mai kyau ga rayuwar ƴan Najeriya.

Daga ƙarshe, ya yi addu’ar cewa:

"Allah Ya sanya wannan wata mai alfarma ya zama na farin ciki da ƙara ƙarfin imani. Sannan Allah ya karɓi ibadun da za a gudanar a wannan watan mai alfarma."

Atiku ya shawarci gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya ba gwamnatin tarayya kan azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Atiku Abubakar ya tura muhimmin sako ga gwamnatin tarayya

Atiku ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta sauƙaƙawa ƴan Najeriya wajen rage musu raɗaɗin halin ƙuncin da suke ya yinda aka fara azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng