Bauchi: Miji Ya Yi Wa Matarsa Dukan Tsiya har Ta Zarce Lahira kan Abincin Ramadan

Bauchi: Miji Ya Yi Wa Matarsa Dukan Tsiya har Ta Zarce Lahira kan Abincin Ramadan

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah, bisa zargin dukan matarsa
  • Ana zargin Alhaji Nura da yi wa Wasila Abdullahi dukan tsiya har ya aika ta lahira a Bauchi da ke Arewa maso Gabas
  • Rikicin ya samo asali ne sakamakon sabani kan kayan abinci da kayan marmari na buda baki, wanda ya rikide zuwa fada tsakanin ma’auratan
  • Bayan dukan, matar ta fadi sumammiya kuma aka garzaya da ita asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta nan take

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani magidanci kan zargin hallaka matarsa da duka.

An zargi mutumin mai suna Alhaji Nuru Isah, mai shekaru 50 ya kashe matarsa, Wasila Abdullahi da bulala.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Miji ya hallaka matarsa da duka kan abincin Ramadan
Wani magidanci ya yi wa matarsa dukan tsiya har lahira a Bauchi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda ango ya rasu ana shirin daura aurensa

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil, shi ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook a yau Lahadi 2 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jihar Bauchi, har ila yau, Legit Hausa ta ruwaito muku yadda ango da yayar amarya suka rasu a wani mummunan hatsarin mota ana saura ƴan mintuna ɗaura aure.

Lamarin ya faru ne a garin Boto da ke jihar Bauchi inda shaidu suka ce hatsarin ya faru ne a lokacin da angon da yayar amaryar ke hanyar zuwa wurin da aka shirya bikin a yankin Tafawa Balewa.

Wani ɗan uwan ango ya ce lamarin ya gigita mutanen Boto musamman amarya wacce ke cike da ƙunci a ranar da aka shirya ɗaura mata aure.

Yan sanda sun cafke wani a Bauchi da ya hallaka matarsa saboda abincin Ramadan
An kama magidanci da ya hallaka matarsa saboda abincin Ramadan. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command.
Asali: Facebook

Yaushe magidanci ya hallaka matarsa a Bauchi?

Ahmad Wakili ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar 1 ga Maris, 2025, da misalin karfe 11:30 na dare a unguwar Fadamam Mada.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake kuma shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 ya rasu

Sabani ya faru sanadin yadda za a sarrafa kayan abinci da kayan marmari na buda baki wanda ya janyo rigima tsakanin Nuru Isah da matarsa ta biyu, Wasila.

Bayan Isah ya buge ta da bulala, ta fadi sumammiya inda aka garzaya da ita asibitin ATBU.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka kan lamarin?

Daga bisani, likitoci suka tabbatar da mutuwar Wasila wanda ya tilasta yan sanda kama mijinta.

Rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan lamarin kamar yadda Kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Muhammad ya tabbatar.

Wannan tsautsayi ya biyo bayan fara azumin watan Ramadan a ranar Asabar 1 ga watan Maris, 2025.

Gwamnatin Bauchi ta rufe makarantu saboda Ramadan

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe makarantun gwamnati da na masu zaman kansu na tsawon makwanni biyar gabanin Ramadan.

Rahotanni sun ce sanarwar ta shafi makarantun firamare har zuwa na gaba da sakandare, yayin da aka ce hutun na cikin jadawalin karatun 2024-2025.

Sai dai kuma, wasu iyaye sun bayyana damuwa cewa hutun Ramadan mai tsawo zai shafi karatun yara, tare da rokon a duba mataki yayin da wasu al'umma su ma ke korafi kan wannan hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel