'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci Wajen Sace Mutane a Neja

'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci Wajen Sace Mutane a Neja

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun ɓadda kama wajen sace mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun yi basaja cikin kayan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar ƙasa (EFCC) sannan suka sace mutane 10
  • Tsagerun ƴan bindigan sun sace mutanen ne a wani otel da ƙaramar hukumar Chanchaga ta jihar Neja bayan sun lalata na'urorin CCTV
  • Jami'an ƴan sanda waɗanda suka tabbatar da aukuwar lamarin, sun bayyana cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye su ba, sun yi basaja cikin kayan aikin hukumar yaƙi da masu aikata cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar ƙasa (EFCC) sun sace mutane a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fusata kan 'yan siyasar da ke siyasantar da rashin tsaro, ya fadi matakin dauka

Ƴan bindigan sun sace mutane 10 daga Otel ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro, a ƙaramar hukumar Chanchaga ta jihar Neja.

'Yan bindiga sun sace mutane a Neja
'Yan bindiga sun sace mutum 10 a Neja Hoto: @HQNigerianArmy (X), @HonBago
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun ɓadda sawu a Neja

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wannan lamarin ya faru ne kusan da ƙarfe 4:58 na safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairun 2025.

Ƴan bindigan sun shiga otel ɗin ne sannan suka yi iƙirarin su jami'an hukumar EFCC ne da suka zo yin wani aiki a hukumance.

An gano cewa waɗanda ake zargin sun lalata na'urar ɗaukar hoton bidiyo ta CCTV ta otel ɗin kafin su shiga ɗakunan da baƙi ke ciki ɗaya bayan ɗaya.

Sun yi awon gaba da mutane 10 daga cikin otel ɗin zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun hallaka 'yan sa kai a Kebbi

Ƴan sanda sun fara gudaɓar da bincike

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda a sashen leken asiri na jihar (Acpol SID), ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma kuɓutar da mutanen da aka sace.

An yi kira ga al'umma da su kasance a ankare da kuma lura da duk wani motsi ko al'amura da ba su dace ba, tare da tabbatar da cewa ana ƙoƙarin ƙara ƙarfafa binciken domin gano abubuwan da ke ɓoye dangane da wannan harin.

Ƴan bindiga sun kai hari a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Neja.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bassa na ƙaramar hukumar Kagara inda suka riƙa bin mutanen har cikin gidajensu suna yin harbe-harbe.

A yayin harin da ƴan bindigan suka kai a cikin tsakar dare, an samu asarar rayukan mutum tara waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel