Ministan Tinubu Ya Yi Hangen Nesa, Ya Gano Hanyar Magance Rashin Tsaro
- Ƙaramin ministan ayyuka na gwamnatin Bola Tinubu, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Muhammad Bello Goronyo ya bayyana cewa samar da ingantattun hanyoyin sufuri zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro
- Ministan ya nuna cewa miyagu suna amfani da hanyoyin da suka lalace wajen aikata muggan laifuka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan ayyuka, Muhammed Bello Goronyo, ya jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na gyaran hanyoyi a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya jaddada cewa inganta hanyoyin sufuri zai taimaka wajen rage matsalar tsaro da kuma ƙarfafa harkokin tattalin arziƙi a duk faɗin Najeriya.

Source: Facebook
Goronyo ya yi wannan bayani ne yayin da yake karɓar wata tawaga daga ƙungiyar matasa don ci gaban Afirika (YOUPAD) a Abuja, inda suka karrama shi da lambar yabo, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Tinubu ya faɗi amfanin hanyoyi
Yayin taron, ministan ya jaddada muhimmancin shirin "Renewed Hope Agenda" na Shugaba Bola Tinubu, yana mai bayyana cewa hanyoyi na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da matsalolin tsaro, musamman ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da mutane.
Ya ce miyagu suna amfani da lalatattun hanyoyi wajen kai hare-hare, don haka samar da hanyoyi masu kyau na da matuƙar tasiri wajen dawo da tsaro.
"Idan akwai hanyoyi masu kyau da za a iya wucewa cikin sauƙi, ayyukan miyagu zai zama mai wahala. Waɗannan ɓata-gari na amfani da lalatattun hanyoyi domin aikata muggan laifuka."
"Wannan ne yasa gwamnatin Tinubu ta sanya gina hanyoyi da gyaransu a gaba, ba wai don haɓaka tattalin arziƙi kaɗai ba, har ma da inganta tsaro a duk faɗin Najeriya."
- Muhammad Bello Goronyo
Ministan ya ƙara da cewa hanyoyin sufuri suna da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar tattalin arziƙi, domin suna saukaka kasuwanci, inganta harkokin sufuri, da kuma buɗe yankunan karkara ga masu zuba jari.
Da yake nuna matukar mamakinsa da wannan karramawa daga ƙungiyar YOUPAD, Goronyo ya sadaukar da lambar yabon ga Shugaba Tinubu da daukacin ƴan Najeriya, yana mai yabawa ƙoƙarinsu kan gaban ƙasa.
An yabi ministan Tinubu
Da yake magana a madadin tawagar, shugaban YOUPAD, Henry Nkem Nwankwo, ya yabawa ministan bisa jajircewarsa wajen kawo ci gaba a fannin ababen more rayuwa,
Ya bayyana cewa an zaɓo shi don wannan karramawar ne bayan yin cikakken bincike kan ayyukansa a muƙaman da ya rike.
Wani wakili daga tawagar, Paul Kwabena, ya bukaci ministan da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da hanyoyi masu inganci a duk fadin Najeriya, yana mai cewa ƙungiyar na fatan ci gaba da aiki tare da ma'aikatar.
Ministan Tinubu ya caccaki mataimakin gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi martani mai zafi ga mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Ministan ya caccaki mataimakin gwamnan kan kalaman da ya yi a kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu dangane da rikicin masarautar Kano.
Asali: Legit.ng

