Fitaccen Basarake kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 Ya Rasu
- Ana cikin alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen basarake a Najeriya da ya shafe shekaru 125 a duniya
- Allah ya yi wa Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar mulki
- Marigayin kafin rasuwarsa, shi ne ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudu
- Za a yi jana'izarsa a gobe Lahadi 2 ga watan Maris, 2025 yayin da Sarakunan Hausawa da malaman addini suka fara zaman makoki a fadarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Fitaccen Basarake wanda shi ne shugaban sarakunan Hausawa a jihohin Kudu 17 ya riga mu gidan gaskiya.
An sanar da rasuwar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, rasuwa bayan ya shafe shekaru 125 a duniya.

Kara karanta wannan
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata

Asali: Original
Yadda aka dakatar da Sarki kan rashin ladabi
Masarautarsa da ke Ibadan a jihar Oyo ita ta sanar da mutuwarsa a ranar Asabar 1 ga watan Maris, 2025, cewar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya, Legit Hausa ta kawo muku labarin cewa an dakatar da Sarkin Sasa sakamakon kama shi da laifin nuna rashin ladabi ga Sarkin Yarbawan kasar Ibadan.
Sannan an yi zargin Sarki Haruna Maiyasin, ya na kulle-kullen tunbuke rawanin wasu masu sarauta tare da nada wasu ba bisa ka'ida ba.
An sa ran dakatar da Maiyasin a wancan lokaci zai dakile barkewar rikici a tsakanin al'ummar Hausawa kamar yadda ya faru a wasu garuruwan a lokutan baya.

Asali: Facebook
An sanar da rasuwar Sarkin Sasa a Ibadan
Sanarwar da Ɗan Masanin Sasa, Alhaji Kasim Ado Yaro, ya fitar ta bayyana cewa marigayin ya rasu a asibiti mai zaman kansa bayan fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa, Sarkin yana riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na yankin Kudu.

Kara karanta wannan
Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai a duniya.
Yaushe aka shirya jana'izar Sarkin Sasa?
An tabbatar da shirin jana'izar marigayin a gobe Lahadi 2 ga watan Maris, 2025 a birnin Ibadan.
Sarakunan Hausawa da malaman addini sun fara zaman makoki a fadarsa da ke Sasa a birnin Ibadan.
An naɗa marigayin basaraken, Alhaji Haruna Maiyasin a matsayin Sarkin Sasa da ke birnin Ibadan tun a shekarar 1981.
An tabbatar da cewa marigayin yana taimakon mutane da kyautar kuɗi, abinci da sutura.
Fitowarsa ta ƙarshe a bainar jama’a ita ce lokacin da ya jagoranci fadawansa zuwa wajen Gwamna Seyi Makinde domin yin ta’aziyya.
Tsohon sanata a Bauchi ya rasu
A baya, kun ji cewa ana cikin alhini bayan tsohon sanatan Bauchi ta Kudu, Lawal Yahaya Gumau, ya rasu a Abuja dalilin gajeriyar rashin lafiya.
Sanata Gumau ya rasu ne da misalin karfe 3:45 na daren ranar Asabar 22 ga watan Faburairun 2025 yana da shekaru 57 a duniya.
Rahotanni sun tabbatar cewa Gumau ya fara zama sanata a 2018 bayan mutuwar Ali Wakili, sai aka sake zabensa a 2019.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng