'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna, Sun Hallaka 'Yan Sa Kai a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna, Sun Hallaka 'Yan Sa Kai a Kebbi

  • Ƴan bindiga sun yi ta'asa bayan sun kai wani harin ta'addanci kan ƴan sa-kai a jihar Kebbi da ke yankin Arewacin Najeriya
  • Tsagerun ƴan bindiga sun yi wa ƴan sa-kan kwanton ɓauna ne bayan sun bi sawunsu domin ƙwato dabbobin da suka sace
  • Jami'an tsaro na sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sanda ne suka gano gawarwakin ƴan sa-kan a cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai guda shida a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar Kebbi.

Ƴan bindigan sun kashe ƴan sa-kan ne a dajin Matankari, bayan da suka bi sahun miyagun ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai a Kebbi
'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa-kai a jihar.Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Atiku Abubakar ya tura muhimmin sako ga gwamnatin tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sa-kai sun bi bayan ƴan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan sa-kan suna bibiyar ƴan bindigan ne bayan satar shanu da aka yi a ƙauyukan Dan Tulu da Rusakde, cikin ƙaramar hukumar Arewa.

Ƴan bindigan waɗanda ba a tantance yawansu ba, sun kai hari a waɗannan yankuna a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 3:30 na dare.

Ƴan bindigan waɗanda suka iso a kan babura kusan bakwai, sun kwashe shanu masu yawa sannan suka tsere zuwa dajin Sokoto.

Bayan aukuwar lamarin, wasu ƴan sa-kai daga Dantulu sun bi sawun miyagun don ƙwato dabbobin da suka sata.

Sai dai a safiyar ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025, ƴan sa-kan sun faɗa tarkon da ƴan bindigan suka kafa, inda suka buɗe musu tare da kashe su baki ɗaya a wurin.

Sojoji sun gano gawarwakin mamatan

Bayan samun bayanan sirri game da harin, dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar ƴan sanda da wasu karin ƴan sa-kai, sun ƙaddamar da aikin bincike a dajin Matankari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashhe mutane, sun sace mutum 100 a jihohin Arewa 2

Da misalin ƙarfe 2:30 na rana tawagar ta samu nasarar gano gawarwakin ƴan sa-kan da aka kashe.

An bayyana sunayen mamatan kamar haka, Lawal Dansida, mai shekara 60, Umaru Dangoje, mai shekara 70 da Ghali. Umaru, mai shekara 35

Sauran sun haɗa da Yakubu Maigeri, mai shekara 53, Hakilu Yusuf, mai shekara 47 da Ishiaka Liman, mai shekara 60.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun ƙara yawan sintiri a yankunan don daƙile sake kai hare-hare, tare da tabbatarwa mazauna yankin cewa za su ci gaba da aiki don dawo da zaman lafiya.

Hukumomi sun kuma gargadi ƴan sa-kai da ka da su dauki matakin kai farmaki ba tare da haɗin gwiwa da jami’an tsaro ba.

Hatsabibin ɗan bindiga ya miƙa wuya a Katsina

A wani labarin kuma,.kun ji cewa wani hatsabibin ɗan bindiga ya miƙa.wuya ga jami'an tsaro a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun tafka gagarumar barna

Ɗan bindigan mai suna Abu Radde tare da yaransa sun ajiye makamansu sannan suka sako mutane 10 da suka yi garkuwa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng