NAHCON Ta Sanar da Fara Daukar Ma'aikata domin Aikin Hajjin 2025
- Hukumar NAHCON za ta fara daukar likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na wucin gadi domin aikin Hajjin 2025 daga ranar 8 ga Maris 2025
- An ruwaito cewa aikin likitocin zai fara tun daga duba mahajjata a Najeriya har zuwa lokacin dawowarsu daga Saudiyya bayan aikin hajji
- An bayyana matakin da masu sha'awa za su dauka domin samun cikakken bayani kan yadda za su nemi aikin kafin lokaci ya kure musu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da shirin daukar likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na wucin gadi domin aikin Hajjin 2025.
Ana sa ran daukar ma’aikatan lafiya ne domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu kulawa daga lokacin shirin tafiya har zuwa lokacin dawowa.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan daukar aikin ne a cikin wani sako da hukumar NAHCON ta wallafa a shafinta na X a yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mariam Zubair Abubakar daga sashen hulda da jama’a na NAHCON ce ta rattaba hannu a kan wata sanarwa da hukumar ta fitar.
Shirin kulawa da lafiya a lokacin Hajji
Duk shekara, Najeriya na tura likitoci da sauran ma'aikatan lafiya domin kula da mahajjata yayin aikin Hajji a Saudiyya.
NAHCON ta bayyana cewa likitoci da ma'aikatan lafiya da za a dauka za su fara aiki tun daga duba lafiyar mahajjata a Najeriya, har zuwa ranakun ibada a Makkah, Arafat da Madinah.
Bugu da kari, aikin likitocin zai ci gaba har sai an tabbatar da cewa dukkan mahajjata sun koma gida lafiya.
Yaushe NAHCON za ta fara daukar ma'aikata?
Hukumar NAHCON ta ce za ta bude shafin daukar aiki daga ranar 8 ga watan Maris, 2025, domin masu sha'awar neman aikin likitanci a Hajji.
Duk wanda ke da sha'awar neman aikin na wucin gadi zai iya ziyartar shafin hukumar a nan domin samun cikakken bayani.

Asali: Facebook
Hukumar ta bukaci kwararrun ma’aikatan lafiya da ke sha'awar aikin su kasance cikin shirin cike takardun neman aiki a lokacin da aka bude shafin domin rajista.
Muhimmancin shirin ga mahajjatan Najeriya
Shirin samar da likitoci a lokacin Hajji yana daya daga cikin manyan matakan da Najeriya ke dauka domin kare lafiyar alhazai.
A kowace shekara, dubban mahajjata na fuskantar matsalolin lafiya sakamakon dimbin jama’a da ke taruwa a wuraren ibada.
Saboda haka, hukumar NAHCON na kokarin tabbatar da cewa ana samar da kulawar lafiya da ta dace ga duk wani mahajjacin Najeriya.
Haka zalika shirin zai taimakawa mutane masu aikin lafiya samun hanyoyin habaka tattali da kwarewar aiki a kasar Saudiyya yayin aikin Hajji.
Saudiyya ta sanar da fara azumi
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta sanar da cewa za a fara azumin watan Ramadan na 2025 a ranar Asabar 1 ga watan Maris.
Saudiyya ta fitar da sanarwar ne bayan kammala duba watan Ramadan a ranar Juma'a bayan cika kwanaki 29 a watan Sha'aban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng