Akpabio: An Tono Yadda Natasha Ta Taba Zargin Omokri da Nemanta da Lalata a 2014
- Bayan zargin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi, an fara tone-tonen abubuwa
- A 2014, Natasha Akpoti ta zargi Reno Omokri da cin zarafinta wanda ya tilasta shi ya fitar da shaidu cewa bai Najeriya
- Rahotanni sun ce a wancan lokaci bayan Omokri ya tabbatar da cewa bai kasa, Natasha ta goge rubutun da ta yi
- Wannan na zuwa ne bayan tayar da kura da zargin Natasha ya yi musamman a kafofin sadarwa na zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An tono yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi Reno Omokri da cin zarafinta tun a shekarar 2014.
Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta yi zargin ne lokacin Omokri yana aiki a matsayin hadimin Goodluck Jonathan.

Asali: Facebook
Zargin Sanata Natasha kan Godswill Akpabio

Kara karanta wannan
'Ba fadanki ba ne': Natasha ta ja kunnen matar Akpabio, ta fadi shirinta kan zarginsa
A watan Oktobar 2021, Natasha ta rubuta a Facebook cewa Omokri ya ci zarafinta a ranar 6 ga Mayu, 2014 a liyafar Uhuru Kenyatta, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zargin Akpabio da Natasha ta yi cewa ya neme ta da lalata amma ta ki amincewa wanda yake amfani da hakan domin hukunta ta.
Natasha ta bayyana yadda Akpabio ke hukunta ta wurin kin karbar kudurorin da ta kawo majalisar domin ci gaba al'umma.
Martanin Akpabio game da zargin Sanata Natasha
Sai dai Akpabio ya yi martani kan zargin inda ya ce kwata-kwata wani abu makamancin haka bai taba faruwa tsakaninsu.
Akpabio ya yi martanin ne ta bakin mai magana da yawunsa, Kenny Okulogbo, inda ya musanta zargin, yana mai cewa karya ce da ba ta da tushe.

Asali: Facebook
Zargin Natasha: Omokri ya bayar da hujjoji
Omokri ya mayar da martani da bayar da kyautar $50,000 ga duk wanda zai kawo hotonsa ko bidiyo daga wannan taron.
Daga baya, Omokri ya fitar da shaidu cewa bai cikin kasar, ya nuna tikitin jirgi da hatimin shige-da-fice na Najeriya da Amurka.
Omokri ya ce a lokacin yana Amurka a matsayin wakilin Jonathan don magance batun 'yan matan Chibok da aka sace.
Abin da Natasha ta yi bayan zargin Omokri
A Amurka, Omokri ya gana da jami’an diflomasiyya kuma an dauke shi hotuna tare da su.
Daga baya, Akpoti ta goge duk wani rubutu da ta yi kan wannan zargi daga shafinta na sada zumunta.
Omokri daga baya ya bayyana cewa an biya shi kudin sulhu a bayan fage domin kawo karshen lamarin.
An zargi Akpabio da cin zarafi a 2020
A baya, kun ji cewa wata tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Joy Nunieh ta fadi yadda ta zabgawa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio mari.
A shekarar 2020, Nunieh ta zargi Akpabio da cin zarafi inda ta ce ta mare shi a gidansa a Apo a Abuja wanda babu macen da ta taba yi masa haka.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne': Matar Akpabio ta yi barazana ga Natasha, ta fallasa tsohuwar alakarsu
Sai dai Sanata Akpabio ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, ya ce an cire Nunieh daga mukaminta ne saboda dalilin rashin da’a da rashin bin tsarin aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng