'Yan Sanda Sun Kai Farmaki Zazzafa, Sun Kama 'Yan Fashi 35 Masu Tare Hanyoyi
- Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Lagos ta kama mutane 35 da ake zargi da fashi da makami a titi a yankunan Ajah da Elemoro
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama su ne a yayin atisayen sintiri da jami'an tsaro suka kaddamar don dakile ayyukan masu laifi
- Kakakin 'yan sandan jihar ya ce ana ci gaba da kai irin wadannan farmaki a jihar don tabbatar da doka da oda da maganain bata gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta sanar da kame wasu mutane 35 da ake zargi da aikata fashin titi a yankunan Ajah da Elemoro.
Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai cewa an kama su ne a cikin mako guda.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an riga an gurfanar da dukkan wadanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukuncin da doka ta tanadar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama 'yan fashi a jihar Legas
A cewar CSP Hundeyin, jami'an rundunar 'yan sanda da ke sintiri a yankunan Ajah da Elemoro ne suka aiwatar da kame mutanen yayin farmakin da suka gudanar.
PM News ta wallafa cewa CSP Benjamin Hundeyin ya ce:
"Wannan aikin sintiri ne da jami'anmu suka kaddamar, musamman a yankin Lekki Phase 1 har zuwa Epe, domin dakile ayyukan masu aikata laifi."
CSP Benjamin Hundeyin ya kara da cewa akwai wasu tawagogin sintiri a sassan jihar Lagos da ke da irin wannan aikin na yaki da miyagun laifuffuka.
Sunayen wasu daga cikin wadanda aka kama
Daga cikin wadanda aka kama a ranar 24 ga watan Fabrairu akwai Alao Oluwafemi, Adeshina Akinrinde, Udoh John, Afolabi Kola, Daniel Augustine, da Olalekan Qudus.
Sauran sun hada da Bashir Umar, Nasiru Muhammed, Ashiru Sanni, John James, Adebayo Oyebode, Aminu Abubakar, Abdullahi Ibrahim da Jamilu Usman.
Dukkan wadannan mutanen sun shiga hannun jami'an tsaro ne a lokacin da ake gudanar da sintiri domin hana aikata miyagun laifuffuka a jihar.

Asali: Getty Images
'Yan sanda sun cigaba da kai farmaki
Da aka tambayi Hundeyin kan yadda suka samu damar kame mutane da yawa a cikin mako guda, sai ya bayyana cewa dukkan tawagogin sintiri suna irin wannan aikin.
CSP Benjamin Hundeyin ya ce:
"Akwai hadin kai kan yadda tawagar 'yan sanda ke sintiri – Dukkansu na aiki ne domin kama masu aikata laifi da tabbatar da cewa an hukunta su."
A cewarsa, rundunar 'yan sanda ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kai farmaki domin dakile ayyukan masu laifi a Lagos.
Jami'an 'Yan sanda sun yi gargadi a Kano

Kara karanta wannan
Jama'a suna zaman ɗar-ɗar, jami'an tsaro da sulken yaki sun kewaye gidan sarki a Kano
A wani rahoton, kun ki cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta yi gargadi yayin da al'ummar jihar suka fara azumin watan Ramadan na shekarar 2025.
'Yan sanda sun bayyana matakan da ya kamata a bi wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin azumi da hanyar da za a bi wajen sanar da su motsin bata gari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng