Ana Neman Turji, Wani Ɗan Bindiga da Yaransa Sun Ba da Mamaki, Sun Mika Wuya

Ana Neman Turji, Wani Ɗan Bindiga da Yaransa Sun Ba da Mamaki, Sun Mika Wuya

  • Yayin da sojoji ke kara kaimi wurin kakkabe yan ta'adda musamman a shiyyar Arewacin Najeriya, wasu rikakku sun mika wuya
  • Fitaccen ɗan bindiga, Abu Radde, da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro, suka saki mutum 10 da suka sace a yarjejeniyar zaman lafiya
  • Majiyoyi sun ce Abu Radde da wasu ‘yan fashi sun nemi sulhu ta hanyar lumana tare da ganawa da jami’ai a Kwari a karamar hukumar Jibia
  • A wurin taron, sun mika bindigogi guda biyu kuma suka saki waɗanda suka sace inda suka ce za su ci gaba da sakin waɗanda ke hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Shahararren ɗan fashin daji, Abu Radde, tare da yaransa, sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Maharan sun tabbatar da neman sulhu inda suka saki mutum 10 da suka sace a yarjejeniyar zaman lafiya da hukumomi suka tsara.

Kara karanta wannan

Ana shirin fara azumin Ramadan, mutane sama da 15 sun mutu a jihar Katsina

Wani fitaccen dan bindiga ya tuba a jihar Katsina
Rikakken dan ta'adda, Abu Radde da wasu yaransa sun nemi sulhu da hukumomi. Hoto: Legit.
Asali: Original

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Katsina

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar cewa Abu Radde da Audu Lankai da Ori da Gila da Adamu Gurbi da Nawagini sun nemi sulhu da hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan harin ta'addanci a karamar hukumar Faskari da ke jihar ana daf da fara azumin watan Ramadan.

Majiyoyi sun ce mazauna yankin sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi awon gaba da wasu mutane da dama da dabbobi bayan hallaka wasu 17.

Yadda 'yan bindiga suka mika wuya a Katsina

An tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka bukaci sulhu da jami'an tsaro sun hada da Umar Black da Margyal da Aloda da yaransu, sun nemi hakan ta hanyar lumana.

A cewar majiyoyi, an gudanar da taron ne a makarantar Kwari da ke karamar hukumar Jibia, inda masu ruwa da tsaki suka tattauna da ‘yan fashin.

Daga bisani, hukumomi sun amince da bukatar yan ta'addan, sai suka ajiye makamansu, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Wsu yan bindiga sun mika wuya a Katsina
Sojoji sun yi nasara bayan karbar tuban wasu rikakkun yan bindiga. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Yadda tubabbun 'yan bindiga suka saki jama'a

A yayin taron, ‘yan bindiga sun mika bindigogi biyu ga sojoji a matsayin alamar yarda da zaman lafiya.

Sannan sun saki mutum goma da suka sace, waɗanda aka kai asibiti don duba lafiyarsu.

‘Yan fashin sun yi alkawarin sakin sauran waɗanda ke hannunsu kuma sun ce ba za su sake kai hare-hare a yankin ba.

Hukumomi sun tabbatar da ci gaba da sa ido da tattara bayanan sirri don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kungiya ta bukaci a ba sojoji goyon baya

Kun ji cewa kungiyar NWYPD ta fadi gudunmawar da yan Najeriya za su ba sojoji domin yaki da ta'addanci da kuma murkushe rikakken dan ta'adda, Bello Turji.

Kungiyar da ke Arewacin Najeriya ta ce ana bukatar hadin kan jama’a don tallafawa sojoji a kokarinsu na yakar Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda a yankin.

Shugaban NWYPD, Salihu Bello shi ya yi wannan roko, ya yabawa kokarin sojoji wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel