'Mulkin Fir'aunanci Ake Yi': Sule Lamido Ya Dura kan APC, Ya Roki Alfarma a Zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce mulkin APC ya yi kamanceceniya da na Fir’auna da aka yi a tarihi
- Sule Lamido ya ce talauci ya zama makami, yunwa kuma tana yawo a titunan kasar wanda ke illa ga al'umma
- Tsohon gwamnan ya bukaci a ba PDP lokaci don sulhunta rikice-rikicenta, ya ce ba jam’iyya kadai ke da alhakin tsawatar wa gwamnati ba
- Ya ce 2027 na iya zama rashin riba ga ’yan Najeriya, saboda jam’iyyun siyasa ba su da manufa, suna son mulki ne kawai ba tare da tsari ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan salon mulkin jam'iyyar APC a Najeriya.
Sule Lamido ya kwatanta mulkin jam'iyyar APC a Najeriya kamar na Fir'auna saboda yadda ya ce ana zaluntar al'umma.

Asali: Facebook
Sule Lamido ya roki yan Najeriya alfarma
Sule Lamido ya bayyana haka yayin wata hira ta musamman da gidan jaridar Tribune, a nan ya tabo lamarin zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya ce yana bukatar yan Najeriya su sake ba PDP dama domin gyara kura-kuranta yayin da take neman sulhu.
Ya ce adawa ba aikin jam'iyyar PDP ba ne kaɗai, har yan Najeriya suna da rawar da za su taka kan haka, cewar Vanguard.
Yadda PDP ke ƙoƙarin sulhunta rigimar cikin gida
Lamido ya ce:
"Ina mamakin yadda kuke mai da hankali kan PDP, mun yi magana da yawa a kai, kuma har ya gundure ’yan Najeriya.
"Ku ba mu lokaci, muna kokarin sulhu, PDP za ta dawo da zaman lafiya da ci gaba.
"Yin adawa ba aikin PDP kadai ba ne, dole ne ’yan Najeriya su tashi tsaye, Gwamnati na su ne, dole su sa ta yin abin da ya dace, idan mutane ba su yarda da mu ba, ba za mu yi tasiri ba."

Asali: Facebook
Lamido ya kalubalanci yan Najeriya kan zaben PDP
Sule Lamido ya kalubalanci 'yan Najeriya, inda ya ce PDP ta gina Najeriya tun 1998, ta dawo da hadin kai bayan mulkin soja.
Ya ce duk waɗanda ake magana suna cikin PDP kafin 2014 Su ne suka rusa jam’iyyar, suka kawo APC mulki.
Ya ce gwamnati na cewa komai yana tafiya daidai, amma a tambayi mutanen Zamfara, Kebbi da Sokoto ko akwai tsaro, a tambayi talakawa ko suna da isasshen kudi.
Game da salon mulkin APC, Lamido ya ce jam'iyyar ta mayar da talauci makami, ta kuma jefa mutane cikin bukata, suna dogaro da tallafi.
Ya ce ya kamata mutane su ki karbar kayan tallafi lokacin zabe, su tsaya tsayin daka domin kwatar ’yancinsu.
Sule Lamido ya shawarci malaman Musulunci
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ba malaman Musulunci shawara kan lamarin siyasa domin tsira da mutuncinsu.
Lamido ya ce malamai sun fara rige-rige da ‘yan siyasa wajen neman mulki a Najeriya maimakon su zama jagororin al'umma da koyar da su addini.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng