Bayan Duba Wata, Sarkin Musulmi Ya Fadi Ranar Fara Azumin Ramadan a Najeriya
- Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da cewa ranar 1 ga Maris, 2025, za ta kasance ranar fara azumin Ramadan na 1446AH a Najeriya
- Sarkin Musulmi ya bayyana cewa rahotanni daga yankuna daban-daban sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a kasar nan
- Ya kuma bukaci al'ummar Musulmi da su gudanar da azumin Ramadan cikin tsoron Allah, tare da yiwa shugabanni da kasar addu'a
- Sarkin Musulmi ya kuma yi kira ga daukacin al'ummar Musulmi da su taimaka wa mabukata ta hanyar bayar da sadaka a wannan wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar lll, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a wasu yankuna na Najeriya.
Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya sanar da daukacin al'ummar Musulmin Najeriya, da su tashi da azumin Ramadana na 2025 a ranar Asabar, 1 ga watan Maris.

Asali: UGC
An ga watan Ramadan a Najeriya
A cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta gani a shafin kwamitin duban wata na Najeriya a dandalin X, Sarkin Musulmi ya ce an tabbatar da ganin watan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da mai alfarma, Sa'ad Abubakar lll ya karanta a bidiyon ta ce:
"A yau Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, wanda ya yi daidai da 29 ga Sha'aban, 1446AH, muka kawo karshen watan Sha'aban.
"Rahotanni na duban jinjirin watan Ramadana, daga sassa daban daban na kasar nan, kuma muka tabbatar da su, sun nuna cewa an ga watan Ramadan.
"Don haka, gobe, 1 ga watan Maris, 2025, za ta zama ranar 1 ga watan Ramadan, 1446AH."
An tunatar da Musulmi falalar Ramadan
Sarkin Musulmi, ya yi kira ga daukacin al'ummar Musulmi da su ribaci watan Ramadan ta hanyar dagewa da bautar Allah da yiwa ƙasa addu'a da shugabanninta.
"Ina kira ga ƴan uwana maza da mata, da su gudanar da azumin wannan shekarar cikin jin tsoron Allah, da kiyaye dokokin da ke tattare da azumin.
"Ina kara nanata mana muhimmancin yi wa shugabanninmu addu'a, da jihohinmu da ma ƙasar mu baki daya."
- Inji sarkin Musulmi.

Asali: Getty Images
Sa'ad Abubakar III ya ce wannan lokaci ne na nuna tausayi da jin ƙai ga mabukata, ta hanyar fitar da sadaka da ba da tallafi ga marasa galihu.
Sarkin Musulmi ya ce:
"Ta hanyar tausaya wa na ƙasa da mu, Allah zai ji tausayinmu, ya amsa addu'o'inmu a wannan wata mai alfarma. Muna rokon Allah ya karbi ibadunmu, Amin."
Kalli bidiyon sanarwar a nan kasa:
An ga watan Ramadana a Saudiyya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta bayyana cewa an ga jinjirin watan Ramadan a yau, Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, daidai da 29 ga Sha'aban, 1446H.
Mahukunta a Saudiyya sun tabbatar da cewa gobe, Asabar, 1 ga watan Maris, 2025, zai zama farkon watan Ramadan na wannan shekara.
Wannan sanarwa ta fito daga hukumar kula da masallatai biyu masu daraja, inda aka umarci Musulmi a Saudiyya su fara azumi gobe Asabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng