'Ba Haka ba ne': Matar Akpabio Ta Yi Barazana ga Natasha, Ta Fallasa Tsohuwar Alakarsu
- Matar Shugaban Majalisar Dattawa, Ekaette Akpabio, ta ce za ta maka Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu kan zargin cin zarafin mata da mijinta ke fuskanta
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa da yi mata tayin lalata yayin wata ziyara da ta kai masa a gidansa a garin Uyo
- Misis Ekaette Akpabio ta musanta zargin, tana mai cewa mijinta mutum ne mai mutunta mata kuma ya dade yana goyon bayansu cikin gwamnati
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Matar Shugaban Majalisar Dattawa, Ekaette Akpabio, ta yi martani ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Ekaette ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan Sanata Natasha game da zargin cin zarafinta da mijinta ke fuskanta.

Asali: Facebook
Zargin da Sanata Natasha ke yi wa Akpabio
Ekaette ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira da aka yi da ita, Sanata Akpoti-Uduaghan ta ce Shugaban Majalisar Dattawa ya yi mata tayin lalata a gidansa da ke birnin Uyo.
Ta ce ya rike hannunta, ya zagaya da ita a cikin gidansa, sannan ya yi mata maganganun da ba su dace ba a gaban mijinta.
Haka kuma, ta ce Akpabio ya nuna cewa idan tana son kudirorinta su samu karbuwa, sai ta amince da buƙatarsa.
Zargin da aka taba yi wa Akpabio a baya
Wannan ba shi ne karon farko da ake zargin Godswill Akpabio da cin zarafin mata ba a rayuwarsa.
A 2020, tsohuwar shugabar rikon kwarya ta NDDC, Joy Nunieh, ta ce Akpabio ya yi mata tayin lalata, amma ta mare shi don kare mutuncinta.
Sai dai Akpabio ya musanta hakan, yana mai cewa wannan zargi karya ne, na batanci kuma ba shi da tushe.

Martanin matar Akpabio kan zargin Sanata Natasha

Kara karanta wannan
Sanata ta yi tone tone kan alakar Natasha da Akpabio, ta fadi fifikon da yake ba ta a majalisa
Ekaette Akpabio ta ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma wata hanya ce ta bata sunan mijinta.
Ta ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma za ta nemi hakkinta a kotu don kare mutuncin mijinta daga irin wannan ikirari, Leadership ta ruwaito.
Ekaette ta ce mijinta mutum ne mai mutunta mata, kuma tun kafin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa yake kokarin ganin mata sun samu matsayi a gwamnati.
Har ila yau, ta ce akwai dadaddiyar alaka mai kyau tsakanin iyalan Akpabio da na Akpoti-Uduaghan kafin Natasha ta auri mijinta.
Sanata Kingibe ta magantu kan zargin Akpabio
Kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar Abuja ta yi magana kan korafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan game da Godswill Akpabio.
Kingibe ta ce ta taɓa shawartar Natasha kan gamuwa da Akpabio a otal bayan ta sanar da ita cewa za su hadu ne a kan wasu matsaloli.
Sanatar ta ce babu wata daga cikin sanatoci mata a majalisa da ta fuskanci cin zarafi, kuma Natasha ba ta taba tuntubar su kan wannan batu ba a lokacin da ya faru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng