Sanata Ta Yi Tone Tone kan Alakar Natasha da Akpabio, Ta Fadi Fifikon da Yake ba Ta a Majalisa

Sanata Ta Yi Tone Tone kan Alakar Natasha da Akpabio, Ta Fadi Fifikon da Yake ba Ta a Majalisa

  • Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar Abuja ta yi magana kan korafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan game da Godswill Akpabio
  • Ireti ta ce sau da yawa ana matsar da ‘yan majalisa mata kamar yadda ake yi wa maza, kuma Natasha ta fi kowacce mace samun gata a wurin Akpabio
  • An ji Sanatar ta ce banu wata daga cikinsu a majalisa da ta fuskanci cin zarafi, kuma Natasha ba ta taba tuntubar su kan wannan batu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sanata Ireti Kingibe ta mayar da martani kan korafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan cewa sauran sanatoci mata uku sun yi shiru game da zargin Godswill Akpabio.

Kingibe ta yi mamaki game da zargin Natasha inda ta ce babu wacce Akpabio ya fi fifita wa kamar ita.

Kara karanta wannan

Natasha: Yadda tsohuwar shugabar NDDC ta mari Akpabio kan zargin lalata a 2020

Sanata Kingibe ta yi fallasa kan alakar Natasha da Akpabio
Sanata Ireti Kingibe ta soki Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zarge-zargenta. Hoto: Godswill Obot Akpabio, Senator Natasha Akpoti-Uduaghan.
Asali: Facebook

'Natasha ta fi kowa gata a wurin Akpabio' - Kingibe

A wata hira, Ireti ta ce ta zabi yin shiru kan lamarin, tana mai cewa, shiru yana da daraja musamman idan ana karya doka, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kingibe ta ce dangane da matsar da kujerar Natasha, babu wacce a majalisa ba a yi wa haka ba.

Ta ce:

“Ina fata matsalar za ta warware da kanta, shi ya sa ban ce komai ba kan Natasha a bainar jama’a."

Ta ce babu wani abu da ake yi wa mata a Majalisa da ba a yi wa maza, don haka ba za a ce mata ake cutarwa ba.

A matsayinta na Shugabar Kwamitin Harkokin Mata, ta ce dole ne mata su bi dokokin Majalisa.

Ta kuma jaddada cewa Natasha ta fi kowacce mace samun gata a cikin Majalisar dattijai ta yanzu.

Sanata Kingibe ta bude aiki game da alakar Natasha da Akpabio

Sanata Ireti Kingibe ta ƙaryata zargin Natasha

Game da zargin cin zarafi da Natasha ke yi wa Akpabio, Ireti ta ce suna da alaka ta kashin kansu tun kafin su shiga Majalisa.

Kara karanta wannan

'Akpabio ya neme ni da lalata': Sanata Natasha ta tona asirin shugaban majalisa

Ta ba da misali yadda ta dauko wasu takardu a Majalisa domin kai wa Natasha a gidanta.

A cewarta, lokacin da suka yi waya, Sanata Natasha ta ce za ta gana da Akpabio a otal don tattauna wata matsala.

Ireti ta ce ta shawarci Natasha da cewa irin wadannan ganawa sun fi dacewa a yi su a ofis ko gida.

Shin da gaske mata na fuskantar cin zarafi?

Da take magana a madadin sauran mata sanatoci biyu, Ireti ta ce ba su taba fuskantar cin zarafi ba.

Sanatar ta kuma ce Natasha ba ta taba tuntubar su kan korafinta ba tun lokacin da lamarin ya faru.

Ta amince cewa Majalisa ba ta cika nuna adalci ga mata ba a baya, amma abubuwa na kara gyaruwa.

Ireti ta soki wannan cece-kuce, tana mai cewa Majalisa ya kamata ta fi mayar da hankali kan dokokin da suka shafi ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi domin cin moriyar watan Ramadan

Yadda tsohuwar shugabar NDDC ta mari Akpabio

A baya, kun ji cewa ana zargin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da cin zarafin tsohuwar shugabar hukumar NDDC.

A shekarar 2020, tsohuwar shugabar NDDC, Joy Nunieh, ta zargi Akpabio da cin zarafi inda ta ce ta mare shi a gidansa a Apo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel