Matsalar Layukan Wutar Lantarki Ta Sake Jefa Fadar Shugaban Kasa a cikin Duhu
- Mazauna wasu yankuna akalla 53 da ke babban birnin tarayya Abuja sun fada a cikin duhu, sakamakon wata matsala da ta afku
- Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja ya tabbatar da afkuwar matsalar a ranar Juma'a, ya ce injiniyoyinta su na aiki tukuru
- Daga cikin wuraren da suka fada a cikin duhu, akwai fadar shugaban kasa, CKC Gwagwalada, Kuje Road, Almat Farms da dai sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - An samu matsalar wutar lantarki a Abuja sakamakon tangardar wasu layukan wuta na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC).
Aƙalla wurare 53 ne matsalar rashin wutar ta shafa, ciki har da Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da kamfanin AEDC ta yi karin bayani a kan matsalar.

Asali: Facebook
Jaridar Punch News ta bayyana cewa wannan tangardar ta hana wuta isowa wasu sassa na birnin Abuja, ciki har da Fadar Shugaban Ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da matsalar wuta a Abuja
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya tabbatar da wannan matsalar wuta a ranar Juma’a.
Kamfanin ya roƙi abokan hulɗarsa da su yi haƙuri yayin da injiniyoyinsa ke aiki ba dare ba rana domin mayar da wuta ga wuraren da matsalar ta shafa cikin gaggawa.
Wuraren da rashin wuta ya shafa a Abuja
A cikin sanarwar da AEDC ya fitar, ya bayyana wasu wuraren da matsalar ta shafa da cewa sun ada da CKC Gwagwalada, Kuje Road, Almat Farms, Kiran Farm, da Efugo.
Sauran wuraren sun haɗa da: Kwali Road, L5 Injection Substation, Chukuku Environs, Premium Farm, El-Rufai Estate, Daghiri, da Kuje Extension.
Sanarwar ta ci gaba da lissafa wasu wuraren kamar haka:
"Cocin living Faith Katampe, kauyen Jahi , Katampe Extension, Jahi by Gilmore, Gishiri, Mabushi, Kadokuchi, Navy Estate, Anan House, dakin taron sojojin sama (NAF), Lake View Phase 1 & 2, Rukunin gidajen Kwastam, Otal din Chida, Dakibiu, Rukunin gidajen Brains and Hammer, Rukunin gidajen Today, Gundumar Dape, Rukunin gidajen sojojin sama, Rukunin gidajen Katsina, Rukunin gidajen Paradise, Rukunin gidajen Ochacho, Gundumar Kafe, Ofishin jakadancin Amurka, wani ɓangare na Gwarinpa, Kwalejin koyon ilmin yaki, Lateef Jakande, Shiyya ta E, Shiyya ta D, Otal din Bestway, da gidan man Eterna.
Abuja: Ana samun yawan samun matsalar lantarki
Matsalar layukan wutar lantarki dai na daga cikin matsalolin dake addabar Abuja sakamakon tsofaffin layukan rarraba wuta da ke buƙatar gyara.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla wurare 188 ne ke ƙarƙashin ikon AEDC a babban birnin tarayyar, kuma suna fuskantar irin waɗannan matsaloli lokaci zuwa lokaci.
TCN ta fadi dalilan yawan matsalar lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana takaicin yadda wasu bata-gari suka dauki gabarar lalata manyan layukan wutar lantarki.
Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ta bayyana wannan lamari, ta ce lalata kayayyakin wuta yana zama babban kalubale ga kamfanin, lamarin da ta ce akwai bukatar jama'a su taimaka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng