Neja: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Musulmai Ana Shirin Fara Azumi, An Rasa Rayuka
- 'Yan bindiga sun kai hari a yankin Karaga, jihar Neja, inda suka kashe manoma tara, sannan suka sace mutane shida da shanu
- Mazauna yankin Bassa, sun bayyana cewa an yiwa mutanen kisan gilla, yayin da 'yan sa-kai ke ci gaba da nemo sauran gawarwaki
- Harin ya zo ne kwana biyar bayan ‘yan bindiga sun kashe mutane 16 a kudancin Neja, lamarin da ke kara tada hankula a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - 'Yan bindiga sun kai hari a Karaga da ke yankin Bassa, karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda suka kashe manoma tara.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun farmaki garin ne da daddaren ranar Laraba, suka rika farmakar mutane a gidajensu.

Asali: Original
Neja: 'Yan bindiga sun kashe manoma 9
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bayan kashe mutane tara, ‘yan bindigar sun sace mutane shida tare da satar shanu masu yawa a yankin Farin-Doki, cikin Shiroro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce an yi wa mutanen kisan gilla, wanda ko kare ba zai ci ba.
Mazaunin yankin ya ce:
"Mun gano gawarwaki tara zuwa yanzu, amma ba mu tabbatar ko akwai wasu karin wadanda suka mutu ba. 'Yan sa-kai na ci gaba da bincike a dazuka.
"Bayan kammala harin Karaga, ‘yan bindigar sun wuce Farin-Doki, inda suka sace mutane shida tare da kwashe shanun da suka fi yawa."
'Yan bindiga sun kai hari Jawu-Farin-Doki
Wata majiya ta kara da cewa 'yan bindigar sun kai farmaki a Juwu-Farin-Doki da ke yankin Erena, duk da cewa babu rahoton rasa rayuka a wajen.
"Halin da ake ciki a Shiroro yana kara tsananta. Mutane na rayuwa cikin tsoro sakamakon hare-haren da ke faruwa akai-akai."
"Harin da aka kai a Karaga da kuma satar da aka yi a Juwu-Farin-Doki sun nuna bukatar gaggawar daukar matakan tsaro a yankin."
- Inji majiyar.
Rahoto ya nuna cewa har yanzu an kasa samun jin ta bakin kwamishinan tsaro na jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya).

Asali: Twitter
Layukan wayarsa ba su shiga ba, kuma bai amsa sakonnin da aka tura masa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce zai yi karin bayani bayan samun cikakkun bayanai, amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada rahoton.
'Mayakan Jihadi' sun kai hari har sau biyu
Harin na zuwa ne bayan kwanaki biyar da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki sau biyu a kudancin jihar Neja, inda suka kashe mutane 16.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ba a tantance wadanda suka kai harin ba, amma irin salon da suka bi na kama da na ‘yan jihadi da ke addabar yankin Sahel.
Rahotanni sun ce maharan sun tattara mutane daga wani kauye a Dioundiou a daren 22 zuwa 23 ga Fabrairu, inda suka bude musu wuta, lamarin da ya yi ajalin 14.
Bayan kwana biyu, wasu ‘yan bindigar sun sake kai farmaki a wani kauyen makwabta, suka kashe mutane biyu.
Yankin Dioundiou, wanda ke iyaka da Najeriya da Benin, na daga cikin wuraren da hukumomin Neja ke cewa ‘yan jihadi sun yi kaka-gida.
'Yan bindiga sun sace mutane da dabbobi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani ƙauyen da ke jihar Neja.
Miyagun 'yan ta'addar sun kai harin ne a ƙauyen Dakpala na ƙaramar hukumar Shiroro, suka sace mutane takwas ciki har da jarirai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng