Bayan Shekaru 2 a Daura, Shettima da Wasu Gwamnoni Sun Raka Buhari Zuwa Kaduna

Bayan Shekaru 2 a Daura, Shettima da Wasu Gwamnoni Sun Raka Buhari Zuwa Kaduna

  • Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya koma jihar Kaduna da zama karon farko tun bayan barinsa mulki
  • Buhari ya koma Kaduna bayan shafe shekaru biyu a arin Daura inda yake zaune tun a karshen watan Mayun 2023
  • Ya samu rakiyar mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da gwamnoni kamar Babagana Zulum na Borno da Uba Sani na Kaduna
  • Bayan isarsa jihar, Buhari ya samu tarba cikin farin ciki daga Malam Mamman Daura da Musa Halilu (Dujiman Adamawa)

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - A yau Alhamis, tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya koma gidansa da ke Kaduna, zai cigaba da zama.

Wannan na zuwa ne bayan shafe shekaru biyu a Daura, Jihar Katsina, tun bayan barinsa mulki a watan Mayun 2023.

Buhari ya bar Daura zuwa Kaduna bayan shafe shekaru 2
Muhammadu Buhari ya samu rakiyar Shettima da sauran gwamnoni zuwa jihar Kaduna. Hoto: @BashirAhmaad.
Asali: Twitter

Bashir Ahmad ya yabawa salon mulkin Buhari

Kara karanta wannan

'Ya ci burin kawar da Kiristocin Kaduna': Hadimin Jonathan ya zargi El Rufai

Tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 27 ga watan Fabrairun 2025 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan tsohon hadimin Buhari ya jawo ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa kan rubutun da ya yi kan salon mulkin mai gidansa.

Bashir Ahmad ya ce salon mulkin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023 ya dara na tsofaffin shugabannin kasa kamar su Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar'adua da kuma Goodluck Jonathan a bangaren manyan ayyuka.

Matashin ya rubuta hakan ne a shafin X, inda yake cewa wadannan shugabanni uku ba su yi abin da Buhari ya yi ba.

Tsawon lokacin da Buhari ya dauka a Daura

A cikin sanarwar, Bashir Ahmad ya ce bayan kammala wa’adinsa, ya zaɓi rayuwa shi kadai inda ya kauce wa harkokin siyasa, yana mai da hankali kan lamuransa na sirri.

Tsohon shugaban ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da manyan jami’ai, ciki har da gwamnoni da waɗanda ke da kusanci da shi.

Kara karanta wannan

'Tsufa ke damunka': NNPP ta dura kan Ganduje da ya ce zai raba Abba da kujerarsa

Buhari ya dira a Kaduna bayan shafe shekaru 2 a Daura
Muhammadu Buhari ya koma gidansa da ke jihar Kaduna. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Wadanda suka raka Muhammadu Buhari zuwa Kaduna

Daga cikin gwamnonin akwai na jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da takwaransa na Kaduna, Uba Sani.

Sannan akwai mataimakan gwamnan Katsina na baya da yanzu, tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda, tsofaffin ministoci, da wasu na kusa da shi.

A Kaduna, Malam Mamman Daura da Musa Halilu (Dujiman Adamawa) da wasu sun hallara don yi masa maraba bayan saukarsa.

Hotunan yadda Buhari ya samu rakiyar manyan mutane

Buhari ya fadi dalilin rashin halartar taron APC

Kun ji cewa bayan ce-ce-ku-ce game da rashin halartar taron jam'iyyar APC da aka gudanar a Abuja, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi martani kan haka.

Hadimin shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa duk da bai halarci taron ba, har yanzu zuciyarsa na tare da jam'iyyar APC, babu abin da zai raba su.

Manyan ƙusoshin APC da suka haɗa da Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi ba su samu halarci taron da aka yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.