Shugaban EFCC Ya Fallasa 'Yan Siyasa da Suka ba Shi Cin Hancin N500m
- Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede ya yi tone-tone kan yadda cin hanci ke kara yawa a Najeriya
- Olukoyede ya fadi yadda ya ƙi karɓar N500m da aka ba shi a lokacin jana’izar mahaifiyarsa a jihar Ekiti a 2019
- Ya bayyana cewa mutane da dama, ciki har da ministoci da shugabannin hukumomi, sun aiko masa da kuɗi da kyaututtuka, amma ya mayar da su
- Shugaban EFCC ya ce ya guji karɓar kuɗin ne don guje wa abin da ka iya zamar masa tarnaki a aikinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja Shugaban Hukumar EFCC, Olanipekun Olukoyede ya bayyana yadda ya tsallake karbar cin hanci daga yan siyasa.
Olukoyede ya ce ya ƙi karɓar fiye da N500m da aka ba shi a lokacin rasuwar mahaifiyarsa a jihar Ekiti.

Source: Facebook
Yadda shugaban EFCC ya ki karbar cin hanci
Olukoyede ya bayyana hakan ne a taron ACSR karo na 38 da aka gudanar a Abuja, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban EFCC ya bayyana yadda ya tsallake tarnaki game da cin hanci da aka kawo masa tun a wancan lokaci.
A cewarsa:
"Na rasa mahaifiyata a 2019 a jihar Ekiti, mun je jana’iza ni ne Sakataren EFCC ne a lokacin.
"Ranar jana’iza, na zo gida sai na tarar da shanu 17 a harabar gidana, a cikin su har da masu ciki.
"Da na isa gida, maigadi na ya kawo mini wata karamar akwati a ciki kuwa sai na ga takardun biyan kudi daga banki da yawa daga jami’an gwamnati."
"Na kai su duka ga matata, ta ce, ‘Alhamdulillah.’ na ce, ‘Alhamdulillah don me?’ da muka ƙirga su, sun kai kusan N500m."

Source: Facebook
Olukoyede ya gargadi masu aiko masa cin hanci
Olukoyede ya ce ya tattara duk takardun inda ya rubuta wasiƙa ga masu aikowa, sannan ya mayar da su don guje wa duk wata matsala a gaba.
Ya kara da cewa:
"An yi jana’izar a watan Satumba 2019, amma zuwa watan Yulin 2020, an bincike ni, idan na karɓi waɗannan kuɗin, me zan ce?"
"Da an ce na karɓi kuɗin ne don jana’izar mahaifiyata, amma wasu daga cikin masu bayarwa na cikin binciken EFCC."
Olukoyede ya ce da ɗan’uwan matarsa ya ji abin da ya yi, ya bar yi masa magana na tsawon wasu watanni shida, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce da har an samu wadannan kudi a bankinsa, da shi ma zai iya tsintar kansa a gidan yari a yanzu.
EFCC sun mamaye ofishin hukumar NAHCON
Kun ji cewa Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, sun yi dirar mikiya a hedkwatar hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ke Abuja.
An ce lokacin samamen da jami'an EFCC suka kai, sun tsare kakakin hukumar NAHCON tare da wasu mutane uku domin gudanar da bincike.
Rahotanni sun ce jami'an sun kai samamen ne a binciken da suke ci gaba da yi kan zargin karkatar da tallafin N90bn da aka ba da a lokacin aikin Hajjin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


