'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, Sun Sace Mutum 100 a Jihohin Arewa 2

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, Sun Sace Mutum 100 a Jihohin Arewa 2

  • Ƴan bindiga na ci gaba da yin ta'asa kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohin Katsina da Zamfara da ke Arewacin Najeriya
  • Miyagun sun hallaka mutum biyar tare da sace mutum 50 a wasu hare-hare da suka kai kan aƙalla ƙauyuka guda 10 na jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan sun kuma kusan kwashe dukkanin mutanen da ke ƙauyen Unguwar Lamido a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a jihohin Zamfara da Katsina.

Ƴan bindigan sun kashe mutum biyar tare da sace fiye da mutum 50 a jerin hare-haren da suka kai a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane a Katsina da Zamfara Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce tun bayan ziyarar babban hafsan sojojin ƙasa a makon da ya gabata, an kai hare-hare a aƙalla ƙauyuka 10 na ƙananan hukumomi shida a Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun tafka gagarumar barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara

Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar tare da sace fiye da mutane 50, waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara.

Ƙananan hukumomin da ƴan bindigan suka kai wa farmaki sun haɗa da Gusau, Bukkuyum, Zurmi, Kaura-Namoda, Maru, da Anka.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kai farmaki a Gusau da Gummi, inda suka kashe yara huɗu, biyu a kowace ƙaramar hukuma tare da sace mutane da dama.

Jaridar Premium Times ta ce mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum, Hon. Bala Muhammad Majidadi, na daga cikin waɗanda aka sace.

Wani mazaunin ƙaramar hukumar Zurmi, Malam Abubakar Zurmi, ya ce ƴan bindigan sun dawo da mummunan ta’addancinsu, bayan sun ɗan lafa na wani ɗan lokaci.

Ya ce duk da yawaitar sintirin sojoji da kuma kashe da dama daga cikin ƴan bindigan, har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare domin sace mutane don karɓar kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun zo da sabon ta'addanci, sun tafka barna a Adamawa

Ƴan bindiga sun yi barna a Katsina

A wani farmaki daban, ƴan bindiga sun sace aƙalla mutum 50 da tsakar rana a Unguwar Lamido da ke ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan suna cin karensu babu babbaka, inda suke kai hare-hare a kowane lokaci ba tare da tsoron hukuma ba.

A harin da suka kai kwanan nan, ƴan ta’addan sun kusa kwashe dukkan mutanen garin, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere zuwa garin Bakori domin tsira da rayuwarsu.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'an ƴan sandan Najeriya sun rasa rayukansu yayin artabu da ƴan bindiga a jihar Plateau.

Jami'an ƴan sandan sun fafata da ƴan bindigan ne sun yi yunkurin sace mutane a yankin Little Rayfield da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

Duk da asarar rayukan da aka samu, ƴan sandan sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindigan na sace mutane a yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng