Bayan Dangote, MRS Ya Rage Farashin Fetur a dukkan Jihohin Najeriya

Bayan Dangote, MRS Ya Rage Farashin Fetur a dukkan Jihohin Najeriya

  • Kamfanin makamashi na MRS ya rage farashin litar man fetur a dukkan gidajen man sa da ke fadin Najeriya
  • Rage farashin ya biyo bayan saukin farashin da matatar Dangote ta yi daga N890 zuwa N825 kan kowace lita
  • Ana ganin matakin a matsayin wani sauki ga ‘yan Najeriya, musamman yayin da watan Ramadan ke karatowa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin MRS ya sanar da rage farashin man fetur a gidajen mai da ke karkashin kulawarsa a fadin Najeriya.

Matakin rage farashin ya zo ne jim kadan bayan matatar Dangote ta rage farashin da take sayarwa ga dillalai, wanda hakan ke nufin ana sa ran karin saukin farashin man fetur a kasuwa.

MRS mai
MRS ya rage farashin fetur a Najeriya. Hoto: @MRSOilNigeria
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan ragi farashin ne a cikin wani sako da kamfanin MRS ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis, 27 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Matatar Ɗangote ta jefa ƴan kasuwa a matsala da ta rage farashin fetur ana shirin Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ganin ragin farashin na cikin kokarin rage radadin hauhawar farashin kaya, musamman yayin da ‘yan Najeriya ke shirin shiga watan azumin Ramadan.

Sabon farashin man fetur na MRS

Kamfanin MRS ya bayyana cewa daga yanzu, za a sayar da man fetur a gidajen mai na kamfanin da farashi kamar haka:

  • Jihar Lagos: N860 kan kowace lita
  • Jihohin Kudu maso Yamma: N870 kan kowace lita
  • Jihohin Arewa: N880 kan kowace lita
  • Jihohin Kudu maso Gabas: N890 kan kowace lita

Kamfanin ya bukaci masu sayen man fetur da su tabbatar da cewa suna siyan mai a wadannan farashin da aka ambata.

Baya ga haka, MRS ya yi gargadin cewa idan wani gidan mai ya sayar da fetur a sama da wannan farashi, a tuntube shi domin daukar matakin da ya dace.

Alakar MRS da matatar Dangote

Kamfanin MRS na daga cikin manyan dillalan da matatar Dangote ta amince su rika sayar da kayanta.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin man fetur, an fara maganar karya farashin siminti a Najeriya

Rage farashin man fetur da Dangote ta yi daga N890 zuwa N825 ya bai wa kamfanoni kamar MRS damar saukaka wa ‘yan kasa ta hanyar rage kudin sayen fetur.

Yayin da matatar Dangote ta rage kudin mai, ta ce:

"Wannan ragin zai taimaka wa ‘yan Najeriya, musamman ganin yadda watan Ramadan ke karatowa."

Saukin farashi ya zama rahama

Masana tattalin arziki na ganin wannan mataki na rage farashin fetur a matsayin wani sauki ga ‘yan Najeriya, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar kayan masarufi.

Haka kuma ana sa ran hakan zai rage kudin sufuri da kuma kara saukin rayuwa ga al’ummar Najeriya.

Al'umma na fatan rage farashin fetur zai taimaka wa jama’a da kuma tallafa wa kokarin da gwamnati ke yi na farfado da tattalin arzikin kasa.

Gidan mai
Motoci na layi a gidan mai. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A yanzu haka dai kallo ya koma kan kamfanin NNPCL domin ganin ko zai bi sahun Dangote da MRS wajen rage farashin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Yadda kayan abinci suka yi sauki a Arewa ana shirin azumi

TInubu ya yi farin ciki da saukar farashi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin ciki da saukar farashin kayan abinci.

Bola Tinubu ya ce abin farin ciki ne yadda farashi ke sauka yayin da ake kokarin fara azumin watan Ramadan na shekarar 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng