Fara Azumi: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Watan Ramadan

Fara Azumi: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Watan Ramadan

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmai su fara duban watan Ramadan daga ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu, 2025
  • Hakan na zuwa ne yayin da ranar Juma'a ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban, 1446 wanda za a iya fara azumi washe gari
  • Fadar Sarkin Musulmi ta bukaci wadanda suka ga watan a fadin Najeriya su tuntube ta ta wasu lambobin wayoyi da ta bayar
  • Wani mazaunin jihar Gombe, Aminu Ahmad ya bayyanawa Legit shirin da ya yi domin duba watan kamar yadda aka bukata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci daukacin Mulmin Najeriya da su fara duban jinjirin watan Ramadan.

Sanarwar da sarkin Musulmi ya fitar da tuna cewa za a fara duba watan ne daga ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa ga musulmi kwanaki 2 kafin fara azumin Ramadan

Sarkin Musulmi
Za a fara duba watan Ramadan a Najeriya. Hoto: National Moon Sighting Committee
Asali: Facebook

Fadar sarkin Musulmi ta wallafa a Facebook cewa wannan rana ita ce ta 29 ga watan Sha’aban, 1446, wacce ke nuna yiwuwar ganin sabuwar jinjirin watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin kula da harkokin addini na majalisar, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar, an bukaci duk wanda ya ga watan ya sanar da majalisar.

Za a fara duba watan Ramadan a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci musulmi su hada kai wajen duba watan Ramadan domin tantance ranar da za a fara azumin shekarar 2025.

A cewar sanarwar da aka fitar, idan an ga watan, ana bukatar a gaggauta sanar da majalisar Sarkin Musulmi a Sokoto domin tabbatarwa da sanar da ranar farko ta azumi.

Duban watan Ramadan ka'ida ce a cikin addinin Musulunci, inda idan an samu tabbacin ganin watan, Sarkin Musulmi ke sanar da al’ummar Najeriya ranar da za a fara azumi.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman kashe wando: Sanata Goje ya raba miliyoyi da kayayyaki

Hanyoyin tuntubar sarkin Musulmi

A cikin sanarwar, an fitar da lambobin waya da za a iya amfani da su wajen kai rahoton ganin watan Ramadan ga majalisar sarkin Musulmi.

An fitar da lambobin da za a iya kira idan an ga watan kamar haka:

📞 08037157100

📞 08066303077

📞 08035965322

📞 08099954903

📞 08067146900

An bukaci duk wanda ya ga watan ya tuntubi wadannan lambobin domin tabbatar da ganin tare da gabatar da bayanai dalla-dalla.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi yana bayanin ganin wata. Hoto: National Moon Sighting Committee
Asali: UGC

An bukaci Musulmi su hada kai

Biyo bayan sanarwar, an bukaci Musulmi su kasance masu biyayya da bin umarnin malamai da shugabanni game da duban watan Ramadan.

Haka zalika an gargadi jama'a da su yi hattara da rade-radin da ba su da tushe, saboda hukuma ce kadai ke da hurumin tabbatar da ganin watan Ramadan.

A karshe, an bukaci musulmi su kasance cikin shiri domin fara azumin watan Ramadan da zarar an samu tabbacin ganin watan daga wurare daban-daban na Najeriya.

Kara karanta wannan

IBB: 'Dalilan kitsa harin rashin imani da ya kashe tsohon shugaban kasa, Murtala'

Legit ta tattauna da Aminu Ahmad

Wani mazaunin jihar Gombe, Aminu Ahmad ya ce zai fito duba watan kamar yadda fadar sarkin Musulmi ta bukata.

Aminu Ahmad ya ce:

"Za mu fita duba watan idan Allah ya yarda, muna fatan Allah ya nuna mana shi.
"Ina fatan Allah ya shigar da mu Ramadan lafiya, ya sa mu kammala azumi lami lafiya."

Ayyukan ibada da za a yi a watan Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya bukaci mutane su dage da ibada a watan Ramadan.

Sheikh Usman Al-Juzuri ya ce Ramadan wata ne mai albarka da ya kamata kowane Musulmi ya yi kokarin cin moriyarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng