Kotu Ta Ba da Belin Farfesa Usman Yusuf, Ta Gindaya Masa Sharuda

Kotu Ta Ba da Belin Farfesa Usman Yusuf, Ta Gindaya Masa Sharuda

  • Rahotanni na nuni da cewa kotu ta ba da belin tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf a ranar Alhamis
  • Hukuma mai yaki da rashawa watau EFCC ce ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf bisa zargin almundahana a ofis
  • Sai dai ya musa zargin da aka yi masa kuma wasu mutane na gani kamar bita da kulli ake yi masa kan sukar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa kotu ta ba da belin tsohon shugaban hukumar inshora ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Hakan na zuwa ne kan yadda aka shafe kwanaki ana gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da ba da belinsa ba, lamarin da ya jawo surutai.

Usman Yusuf
An ba da belin Farfesa Usman Yusuf. Hoto: Muhammad Kime
Asali: Twitter

Dan gwagwarmaya, Mahadi Shehu ne ya wallafa matakin ba da belin da kotun ta dauka a wani sako da ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Najeriya ta kafa tarihin kera jirgi a karon farko, zai fara tashi sararin samaniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al'umma daga Arewacin Najeriya sun caccaki gwamnatin tarayya kan kama Farfesa Yusuf suna masu cewa bita da kulli ake masa saboda sukar tsare tsaren Bola Tinubu.

Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Bauchi, Ladan Salihu ya wallafa a X cewa alkalin kotun ya ce sharudan masu sauki ne da za a iya cika su cikin kankanin lokaci.

Yadda zaman kotu ya gudana a yau

A lokacin zaman kotu, Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa bai aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su ba.

Lauyan da ke kare shi, O.I. Habeeb (SAN), ya nemi kotu ta bayar da belinsa, yana mai cewa laifuffukan da ake zarginsa da su suna da damar beli.

Sai dai lauyan EFCC, Francis Usani, ya yi tir da batun bayar da belin, yana mai cewa Farfesa Yusuf ya saba sharudan belin da aka sanya a ofishin EFCC.

Usani ya kuma bayyana cewa Farfesa Yusuf yana ikirarin yana da karfi a fagen siyasa kuma akwai yiwuwar ya tsere idan an sake shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Lauyan ya ce:

“Dole EFCC ta yi bincike mai zurfi da kuma amfani da dabaru na sirri kafin a samu cafke shi,”

Matakin da kotu ta dauka

Bayan sauraron dukkan bangarorin biyu, mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta bada umarnin sakin Farfesa Yusuf idan ya cika sharudan belin da kotu ta gindaya.

Daily Trust ta wallafa cewa har yanzu shari’ar za ta ci gaba, kuma ana sa ran sauraron karin bayanai a zaman kotu na gaba.

Farfesa Yusuf
An zargi Farfesa Yusuf da almundahana. Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta bayar da belin a ranar Alhamis, inda ta bada umarnin sakin Yusuf daga gidan gyaran hali na Kuje idan ya cika sharudan belin da aka gindaya masa.

Farfesa Usman Yusuf ya ce ba gudu ba ja da baya a kan gwagwarmayar da ya fara, kuma ya mika godiya ga wadanda suka tsaya masa a dukkan sassan Najeriya.

EFCC ta kai samame ofishin NAHCON

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar EFCC sun kai samame ofishin hukumar alhazai ta kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i ya fadi kalubalen da za a fuskanta wajen tallar Tinubu a Arewa

Bayanan da aka samu sun nuna cewa EFCC ta kai samamen ne sakamon zargin cin hanci da rashawa da ta ke yi wa wasu jami'an hukumar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng