Gwamna Zulum zai Koya wa Talakawa Neman na Kai a Jihar Borno

Gwamna Zulum zai Koya wa Talakawa Neman na Kai a Jihar Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin da zai taimaki mutanensa wajen dogaro da kai
  • Ya bayyana cewa an yi shirin rage yawan tallafin da ake raba wa talakawan jihar, za a mayar da hankula wajen taimaka wa kananan hukumomi biyu
  • Gwamna Zulum ya kara da cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin da jama'ar da za a daina ba wa tallafin za su samu saukin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa ta rage yawan tallafin abinci.

Ya bayyana cewa za a yi ragin ne da 90% na rabon tallafin abinci domin karfafa wa mazauna jihar gwiwar dogaro da kai.

Kara karanta wannan

"Tsintsiya madaurinki daya mu ke," Gwamnan APC ya yi watsi da zargin El-Rufa'i

Borno
Za a rage raba tallafin abinci a Borno Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Borno za ta fi mayar da hankali kan daukar matakan ci gaba na dogon zango a maimakon raba tallafi yau da gobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin kaddamar da rabon kayan abinci ga gidaje 25,000 a Maiduguri, Jere da wasu sassan jihar, a gabanin watan Ramadan.

Zulum ya fadi amfanin ayyukansa a Borno

Business day ta ruwaito cewa gwamnan ce gwamnatinsa ta saka hannun jari mai yawa domin tallafawa sama da manoma miliyan daya da kayayyakin aikin gona.

Babagana
Za a mayar da hankali wajen tallafa wa kananan hukumomi 2 Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Daga cikin kayayyakin da aka rabawa manoma akwai iri, taki, injinan ban ruwa, magungunan kwari da na kashe ciyawa masu guba a gonakinsu.

Zulum ya ce:

“Wannan tsari ba wai kawai zai karfafa dogaro da kai ba, har ila yau, zai rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa.”

Gwamnatin Borno za ta rage rabpm tallafi

Gwamnan ya kara da cewa daga shekarar 2025, rabon tallafin abinci zai tsaya ne kawai a kananan hukumomi biyu daga cikin 27 da ke jihar, saboda matsalolinsu na musamman.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa

Gwamna Zulum ya ce:

“Kawai kananan hukumomin da za su ci gajiyar rabon tallafin abinci su ne Ngala da Kala-Balge, saboda yanayinsu na musamman.
“Wadannan yankuna sun fuskanci babbar matsalar lalacewar gonaki sakamakon mamayar giwaye, tare da iftila’in ambaliya.
Don haka, a shekarar 2025, gwamnatin jihar Borno za ta samar da tallafin abinci ne kawai ga Ngala da Kala-Balge.”

Zulum ya jaddada cewa duk da matsalar ambaliya, manoma a fadin jihar da suka hada da masu noma a damina da na rani, sun samu dimbin amfanin gona.

Majalisa ta damu da rashin tsaro a Borno

A baya, kun samu labarin cewa majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar Borno.

Majalisar ta bukaci a tura karin jami’an tsaro zuwa jihar don dakile hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa al’ummar yankin da sassan Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

Wannan matsaya ta biyo bayan gabatar da kudirin gaggawa daga dan majalisa mai wakiltar Askira-Uba/Hawul daga Borno, Midala Balami, na jam’iyyar PDP biyo bayan ta'addanci a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.