'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Zo da Sabon Ta'addanci, Sun Tafka Barna a Adamawa
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai sabon harin ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
- Miyagun ɗauke da muggan makamai sun ƙona gidaje, makarantu da shaguna tare da sace dukiyoyin miliyoyin Naira a harin da suka kai cikin dare
- Dakarun sojoji sun kai ɗauki bayan samun rahoton kai harin, inda suka yi artabu da ƴan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Wasu ƴan ta’addan Boko Haram ɗauke da manyan makamai sun kai farmaki cikin dare a jihar Adamawa.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a garin Kwapre da wasu ƙauyuka a yankin Sabuwar Yadul da ke ƙaramar hukumar Hong a Adamawa.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin wanda ya fara da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, ya ɗauki tsawon lokaci har zuwa cikin dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Boko Haram sun yi ɓarna a Adamawa
Bayan sun bar yankin, an gano cewa ƴan ta'addan na Boko Haram sun ɓarnata abubuwa masu tarin yawa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta’addan sun banka wuta ga wuraren ibada, makarantu, gidaje da shaguna, tare da sace dukiyoyi da suka kai miliyoyin Naira.
Dagacin Kwapre, Mista Joel Kulaha, da Dagacin King, Abalis Jawaja, sun ce maharan sun mamaye ƙauyukansu, inda suka ƙona gine-gine, sannan suka kwashe dukiyoyi masu yawa.
Sai dai, a cewar shugabannin ƙauyukan, babu asarar rai a harin, domin mazauna yankin sun samu labarin barazanar hare-haren tun kafin maharan su iso, lamarin da ya basu damar tserewa.
“Muna godiya ga Allah saboda mun tsira da rayukanmu, amma komai namu ya salwanta."
- Joel Kulaha
Sojojin Najeriya sun kai ɗauki
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojoji da ke sansanin Garaha sun yi ƙoƙarin kai ɗauki bayan samun labarin harin.
Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan, wanda hakan ya tilastawa maharan janyewa.
Duk da haka, mazauna yankin sun ce dakarun sojojin sun zo a makare, domin kafin su iso, maharan sun riga sun aikata ɓarna mai girma, ta hanyar lalata gine-gine da sace dukiyoyi.
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojojin runduna ta 23, A. S. Adewunmi, bai kai ga nasara ba.
Kakakin rundunar bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aike masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.
Ƴan Boko Haram sun yi ɓarna a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haram sun sanya ababen fashewa a jihar Borno.
Aƙalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu ababen fashewa lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa domin neman na kansu.
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce motar da mutanen ke ciki ce ta taka bam ɗin, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng