El Rufa'i Ya Fadi Yadda Aikin Ribadu Ke Taimaka wa 'Yan Ta'adda da Miyagun Makamai
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi zargin cewa ana ba da kudin fansa domin a sako waɗanda aka yi garkuwa da su
- Ya fadi haka ne a martani kan sace shugaban Fulani da wasu mutum 38 a jihar Kaduna a kwanan nan, inda ya ce akwai shirin ceto su
- El-Rufa’i na zargin mashawarcin shugaban kasa, Nuhu Ribadu da Uba Sani da yi wa lamarin tsaro a Kaduna, rikon sakainar kashi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana yadda ake ceto wasu daga cikin ‘yan Najeriya da ‘yan bindiga ke garkuwa da su, musamman a jiharsa.
El-Rufa’i ya yi zargin cewa ana biyan ‘yan ta’adda kudin fansa, sannan a mika su ga gwamnatin jihar Kaduna, karkashin gwamna Uba Sani.

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan ya wallafa wannan a shafinsa na X, a matsayin martani ga wani sako da Yusuf Tukur PhD ya aika kan sace jagoran Fulani a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Tukur PhD, ya wallafa a shafinsa cewa an yi shiru a kan batun sace shugaban Fulani da wasu mutum 38 a jihar Kaduna saboda ba El-Rufa’i ne ke mulki ba.
El-Rufa’i: “Ana taimakawa ‘yan ta’adda”
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana damuwa kan yadda ayyukan masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro ke kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a jihar.
El-Rufa’i ya ce akwai matsala a yadda gwamnatin Kaduna da ofishin mashawarcin shugaban kasa, karkashin jagorancin Nuhu Ribadu, ke tafiyar da yaki da ‘yan ta’adda.
El-Rufa'i ya zargi Ribadu da wasa da tsaro
Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa biyan kudin fansa yana taimakawa wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da wuri.

Asali: Facebook
A kan mutanen da aka sace a baya-bayan nan, tsohon gwamnan ya bayyana yakinin cewa za a yi kokarin biyan kudin fansa domin ceto su da wuri.
Ya ce:
"Za a biya ‘yan bindiga kudin fansa domin su sako su da wuri, sannan NSA zai mika waɗanda aka ceto ga gwamnatin jiha cikin wani biki mai kayatarwa."
"Yaudara ta fi shugabanci mai ma’ana a mulkin nan. Da haka ake ƙara wa 'yan ta'adda ƙarfin kuɗi, kuma za su sayi makamai masu kyau don su ci gaba da sace mutane a Kaduna da wasu wurare."
El-Rufa'i: "Babu abota a tsakani na da su"
A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya zargi Uba Sani da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da cin dunduniyarsa.
Ya kara da cewa wannan ce ta sa yanzu haka, suka raba gari, inda ya yi takaicin yadda ya ce, Ribadu ya na jagorantar kwantar da siyasarsa a Najeriya a shirin da ya ke kan zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng