'Saboda Ramadan': Dangote Ya Duba Halin da Ake ciki, Ya Sake Rage Farashin Fetur
- Matatar man Alhaji Aliko Dangote ta sake rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 kowace lita
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an a ranar 26 ga Fabrairu 2025 a Lagos inda za a siyar da lita kan ₦860
- Farashin fetur a AP da Heyden zai kasance ₦865 a Lagos, ₦875 a Kudu maso Yamma, sai kuma ₦885 a Arewa
- Matatar Dangote ta ce rage farashin zai taimaka wa ’yan Najeriya, musamman gabanin Ramadan, tare da tallafa wa manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Hukumar gudanarwar matatar Aliko Dangote ta sanar da rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 kowace lita.
Sanarwar da matatar ta fitar ta tabbatar da cewa matakin zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 27 ga Fabrairu 2025.

Kara karanta wannan
IBB: 'Dalilan kitsa harin rashin imani da ya kashe tsohon shugaban kasa, Murtala'

Asali: UGC
Ramadan: Matatar Dangote ta rage farashin fetur
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Laraba 26 ga watan Fabrairun 2025 a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, an bayyana cewa a Lagos, gidajen mai na MRS za su sayar da fetur kan ₦860 kowace lita.
Sanarwar ta ce:
“Gidajen mai na MRS za su sayar da kowace lita kan ₦860 a Lagos, ₦870 a Kudu maso Yamma, ₦880 a Arewa, da ₦890 a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
“Haka kuma, a gidajen mai na AP da Heyden, fetur zai kasance ₦865 a Lagos, ₦875 a Kudu maso Yamma, ₦885 a Arewa, da ₦895 a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.”

Wane tabbaci matatar Dangote ta ba yan Najeriya?
Kamfanin ya tabbatar wa jama’a da wadatar fetur a kasuwa, tare da isasshen kaya don biyan bukatar cikin gida da kuma fitar da ragowar kasashen waje.
Ya bukaci ’yan kasuwa su goyi bayan wannan mataki don tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun fi cin gajiyar rage farashin fetur.
Kamfanin ya ce rage farashin fetur zai rage radadin tattalin arziki, musamman gabanin Ramadan, tare da taimakawa manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Dangote ya saba rage farashin man fetur
Aliko Dangote, wanda shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, ya rage farashin fetur a lokuta da dama a baya.
Wannan shi ne karo na biyu da aka rage farashin fetur a Fabrairun 2025, bayan ragewa da N60 da aka yi a farkon watan.
A Disamba 2024, yayin bikin Kirsimeti, kamfanin ya rage farashin fetur da ₦70.50, daga ₦970 zuwa ₦899.50, domin saukaka rayuwa ga ’yan Najeriya.
Kalubalen da Dangote ya fuskanta a rayuwa
Kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya fadi irin kalubalen da ya fuskanta da matsin lamba daga wasu mutane da ke kokarin hana nasarar matatar man fetur dinsa.
Fitaccen dan kasuwar ya ce da aikin matatar ya gaza kammaluwa, da shi kansa ya rasa komai a duniya, kasancewar ya saka jari mai yawa a ciki.
Dangote ya jaddada cewa dole ne Afrika ta fara dogaro da kanta wajen sarrafa albarkatun da take da su maimakon shigo da kayayyaki daga kasashe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng