Tashin Hankali: An Janye Dukkanin Jami'an Tsaron da ke Gadin Kakakin Majalisa
- An janye dukkanin jami’an tsaron da ke kula da shugabar majalisar jihar Legas, Mojisola Meranda, lamarin da ke barazana ga tsaronta
- Wani hadimin Rt. Hon. Mojisola Meranda ya bayyana cewa an janye dukkanin jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da na DSS
- Wannan na zuwa ne yayin da magatakardar majalisar da aka tsige yayi yunkurin komawa ofishinsa, lamarin da ya jawo hatsaniya a ranar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Rikicin da ke gudana a majalisar jihar Legas ya dauki sabon salo bayan an janye dukkanin jami’an tsaron da ke gadin shugabar majalisar, Mojisola Meranda.
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin shugabanci a majalisar, lamarin da ke barazanar kawo rashin tsaro ga kakakin majalisar.

Asali: Twitter
An bar shugabar majalisa babu tsaro

Kara karanta wannan
Bayan kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje sun kira taron kusoshin APC a Abuja
Wani hadimin shugabar majalisar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa jaridar Vanguard cewa an janye jami’an tsaron da suka hada da ‘yan sanda da DSS da safiyar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin ya ce:
"A safiyar Alhamis muka tashi da abin mamaki, domin mun gano cewa an janye dukkanin jami’an tsaron da ke kula da kakakin majalisa, Mojisola Meranda.
"Wannan ya hada da ‘yan sanda da DSS, lamarin da zai jefa ta a rashin tsaro, musamman a wannan lokaci na rikicin shugabanci."
Punch ta ruwaito hadimin ya bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya hanzarta daukar matakin da ya dace domin hana barkewar rikici a majalisar.
An hana tsohon magatakardan majalisa shiga ofis
Wannan na zuwa yayin da a ranar Laraba, Olalekan Onafeko, tsohon magatakardan majalisar da aka dakatar, ya yi kokarin komawa ofishinsa.

Asali: Twitter
Sai dai, jami’an tsaro sun dakatar da shi cikin lumana tare da hana shi shiga harabar majalisar.

Kara karanta wannan
Jerin Majalisun dokoki na jihohi 6 da aka sha fama da rikicin shugabanci a Najeriya
An ruwaito cewa Onafeko, wanda aka cire tare da tsohon shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya iso harabar majalisar da karfe 9:00 na safe, tare da lauyansa, jami’an tsaro biyu da wasu jami’an DSS.
"An shawarci magatakardar da aka dakatar da ya fice cikin lumana daga harabar majalisar, tun da dai ana sauraron karar da ke gaban kotu," in ji wani ganau.
Ma'aikatan majalisar Legas sun yi Allah-wadai
A wani faifan bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an hangi ma’aikatan majalisar suna yi wa Onafeko ihun rashin amincewa yayin da ake korar sa daga harabar majalisar.
Biyo bayan lamarin, majalisar Legas, ta hannun babban jami'in tsaron majalisar, Kushoro Idowu ta fitar da wata sanarwar Allah-wadai da matakin Onafeko.
DSS ta maye zauren majalisar Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) dauke da makamai sun mamaye zaure da ginin majalisar dokokin Legas.
An ce jami'an tsaron sun kuma garkame ofisoshin shugabar majalisar Mojisola Meranda, mataimakinta da sakataren majalisa.
Wata sanarwa daga majalisar Legas, ya nuna cewa, 'yan majalisar sun bayyana matakin da DSS ta dauka a matsayin cin zarafin dimokuradiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng