Da Gaske Tinubu Ya Fara Korar Amurkawa 700 da Hana Amfani da Wayoyinsu a Najeriya?
- Kafofin sada zumunta sun cika da rade-radin cewa Bola Tinubu ya fara korar Amurkawa 700 daga Najeriya tare da hana amfani da wayoyinsu
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnati ta ce akwai ‘yan Najeriya 201 a sansanonin shige da ficen Amurka da ake shirin dawo da su gida
- Sai dai binciken da aka gudanar ya gano cewa babu wata hujja da ta nuna Tinubu ya fara korar Amurkawa ko hana amfani da wayoyinsu a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kafafen sada zumunta sun cika da rahotannin da ke nuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara korar Amurkawa 700 daga Najeriya.
Wani hoto da ake yadawa game da wannan ikirarin, sun kuma nuna cewa Shugaban kasa Tinubu ya haramta amfani da wayoyin Amurka a Najeriya.

Asali: Getty Images
Ana zargin Tinubu ya fara korar Amurkawa
Wani Small Daddy ne ya wallafa wannan hoton da ake magana a kansa a ranar 25 ga Janairu, 2025, a shafinsa na Facebook, daga shafin X na wani Celebrity Blogger.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sakon, matakin Tinubu martani ne ga tsauraran dokokin shugaba Donald Trump kan ‘yan gudun hijira a Amurka.
Daga bisani, sakon ya bace daga shafin, amma hotunan sakon suna ci gaba da yaduwa a kafofin sada zumunta.
Dokar Trump da ke barazana ga bakin haure
Tun bayan hawansa mulki a ranar 20 ga Janairu, Trump ya rattaba hannu kan wasu dokoki domin aiwatar da shirin tasa keyar bakin haure.
Dokokin gaggawa da Trump ke rattabawa hannu, suna ba shi damar daukar matakan doka kai tsaye ba tare da amincewar majalisa ba.
Wata takarda daga hukumar shige da fice ta Amurka (ICE), ta nuna cewa sama da mutane miliyan 1.4 ne za a kora daga kasar.
Cikin adadin da ke fuskantar barazanar korar, an ce akwai sunayen ‘yan Najeriya 3,690 a cikin jerin sunayen mutanen da ICE ke shirin koro su gida.
ICE ita ce hukuma mai kula da dokokin shige da fice, iyakoki, cinikayya da kuma ka’idojin shigar baki a Amurka.
Babu hujjar Tinubu na korar Amurkawa

Asali: Twitter
Amma shin, da gaske ne Tinubu da ya fara korar Amurkawa daga Najeriya ko kuma ya haramta amfani da wayoyin Amurka?
Binciken da Africa Check ta gudanar bai gano wata majiyar gaskiya da ke tabbatar da wadannan ikirari ba.
Idan da hakan gaskiya ne, jaridun duniya da na cikin gida za su ruwaito hakan cikin gaggawa.
Shafin X da ya fara yada labarin bai bayar da wata hujja ko majiyar da ke tabbatar da sahihancin bayanan ba.
A ranar 17 ga Fabrairu, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa akwai ‘yan Najeriya 201 a sansanonin shige da fice na Amurka.
Cikin wadannan mutane, an riga an tantance 85 daga domin mayar da su Najeriya daga Amurka.
Najeriya ta cafke bakin haure
A ranar 18 ga Fabrairu, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta cafke bakin haure 40 a jihar Oyo.
A cikin mutanen da aka kama, akwai ‘yan Kamaru 27, ‘yan Ghana biyu, ‘yan Benin 10, da kuma dan Togo daya.
Babu wata sanarwa daga gwamnatin Najeriya ko hukumar NIS da ke nuna cewa akwai Amurkawa da ke zama ba bisa ka’ida ba a kasar.
Hakazalika, babu wata shaida da ke tabbatar da cewa an haramta amfani da wayoyin da aka kera a Amurka a Najeriya.
'Yan Najeriya sun fara buya a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriya sun daina fitowa fili saboda fargabar kama su da korar su daga Amurka bayan Donald Trump ya tsaurara matakai.
Rahotanni sun nuna cewa kusan 'yan Najeriya 3,690 na fuskantar barazanar kora daga Amurka bisa zargin zama ba bisa ka'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng