Jonathan Ya Tuna Baya, Ya Fadi Abin da Ya So Haddasa Rikici a Najeriya

Jonathan Ya Tuna Baya, Ya Fadi Abin da Ya So Haddasa Rikici a Najeriya

  • Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sake taɓo batun zaɓen shekarar 2015 da ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari
  • Goodluck Jonathan ya bayyana cewa na'urar tantance katin zaɓe da INEC ta fito da ita a lokacin, ta kusa haddasa rikici a Najeriya
  • Tsohon shugaban ƙasan ya nuna cewa na'urar ta ƙi karɓarsa da shi da iyalinsa sannan ta kusa jawo hatsaniya a cikin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya sake yin magana kan zaɓen 2015 da ya sha kaye a hannun magajinsa, Muhammadu Buhari.

Goodluck Jonathan ya ce na’urar tantance katin zaɓe ta ƙi karɓarsa shi da matarsa da mahaifiyarsa, sannan ta kusa haddasa rikici a Najeriya.

Jonathan ya yi magana kan zaben 2015
Jonathan ya yi tsokaci kan zaben 2015 Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ƙungiyar YIAGA Africa ta shirya kan zaɓuka a yankin Afirika ta Yamma, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa, Jonathan ya fallasa yadda ake murɗe zaɓe a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya faɗi hanyar samun sahihin zaɓe

Goodluck Jonathan ya ce nasarar kowanne zaɓe na da nasaba da yadda hukumar zabe da ƴan sanda suka gudanar da shi.

“A kullum ina da ra’ayin cewa nasara ko faɗuwar kowanne zaɓe yana hannun manyan hukumomi guda biyu, hukumar zaɓe da kuma ƴan sanda."
"Babu tantama, zaman lafiyar kowacce dimokuradiyya na da alaƙa da yadda ake gudanar da zaɓe da kuma kula da tsaronsa."
"Idan har ba a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci ba, hakan na iya rage sahihancin tsarin zaɓen da kuma halaccin gwamnati gaba ɗaya."

- Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban ƙasan ya jinjinawa matasa kan yadda suke ƙara taka rawa a harkar zaɓe, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar nasara.

Jonathan ya tuna da zaɓen 2015

Duk da haka, Jonathan ya tuna yadda na'urar da hukumar INEC a ƙarƙashin tsohon shugabanta, Farfesa Attahiru Jega, ta kawo ta ƙi karɓarsa shi da iyalinsa.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Tinubu ya fadi kudaden da ake ba gwamnonin Najeriya

Idan za a tuna, a zaɓen 2015 ne shugaban ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.

A yayin da yake bayyana abin da ya faru cikin raha, Jonathan ya ce:

“Lokacin da Jega ke rike da INEC, ya kawo na’urar tantance katin zaɓe. Amma lokacin zaɓe, na'urar ta ƙi karɓa ta, ta kuma kusa haddasa rikici a ƙasa."
"Domin kuwa na’urar ta ƙi karɓa ta, ta ƙi karɓar matata, ta ƙi karɓar mahaifiyata.”

Sai dai duk da waɗannan matsalolin, ya ce sanya fasahar zamani a harkar zaɓe a ƙasashen yammacin Afirka na da matuƙar muhimmanci.

Jonathan ya yabi Muhammadu Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya taya Muhammadu Buhari murnar cika shekara 82 a duniya.

Jonathan ya yi wa tsohon shugaban ƙasan fatan samun lafiya da kwanciyar hankali a saƙon da ya aika masa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Attahiru Jega ya gano matsalar dimokuradiyya a Afirika, ya fadi mafita

Goodluck Jonathan ya kuma kwararo yabo ga Muhammadu Buhari kan yadda ya kawo ci gaba da haɗin kai a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng