Gwamna Abba Ya Tasamma Kare Kambunsa, Ya Dauko Aikin Gina Makarantu sama da 100

Gwamna Abba Ya Tasamma Kare Kambunsa, Ya Dauko Aikin Gina Makarantu sama da 100

  • Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta bayyana takaici a kan halin da ta samu ilimi bayan ta karbi mulki shekara guda da ta gabata
  • Kwamishinan ilimi na Kano, Dr. Ali Haruna Makoda ya ce wannan ne ya zaburar da gwamnatin wajen daukar matakan gyara sashen a fadin jihar
  • Daga cikin matakan da aka dauka, ana shirin gina sababbin makarantun sakandare domin kawo gyara ga cunkoson dalibai da lalacewar wasu makarantun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoKwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayyana shirin gina sabbin makarantu 130 a fadin jihar ta shirin inganta ilimin yara mata na AGILE.

Dr. Ali Makoda ya ce wannan gini zai kunshi makarantu 75 na karamar sakandare da kuma makarantu 55 na babbar sakandare a dukkan sassan jihar.

Kara karanta wannan

Abba ya zama gwamnan gwamnonin Afrika, an gwangwaje shi a kasar waje

Jihar Kano
Gwamnatin Kano zai gina makarantu 130 a fadin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa kwamishinan ya bayyana shirin gwamnatin jihar na gabatar da manhajojin koyar da fasahar zamani domin tabbatar da ingantaccen ilimi a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba na takaicin watsi da ilimi

Jaridar Punch ta wallafa cewa Dr. Makoda ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da bangaren ilimi, abin da ya haifar da lalacewar gine-ginen makarantu.

Ya kuma bayyana wasu matsalolin da ke addabar fannin ilimi a Kano, wadanda suka hada da cunkoson dalibai a ajujuwa da kuma karancin malamai.

Abban Kanawa
Gwamnatin Kano ta fusata da yadda ta samu sashen ilimi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kwamishinan ya gode wa hukumomin ci gaba bisa gudunmawar da suke ba wa bangaren ilimi a jihar,.

Ya kara da ba da tabbacin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da ba su goyon baya domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Gwamnatin Kano ta yi taro kan ilimi

Dr. Makoda ya kuma bayyana cewa Kwamitin Hadin Gwiwa kan Ilimi na Jihar Kano ya gudanar da taron kwanaki biyu a Kaduna domin duba manyan abubuwan da suka shafi fannin ilimi na shekarar 2025-2026.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

Taron da aka fara daga Asabar 22 zuwa Lahadi 23 ga watan Fabrairu 2025, ya mayar da hankali a kan daidaita manufofi da tsare-tsaren ilimi na jihar domin samun sakamako mai inganci.

Hon. Makoda ya bayyana cewa taron yana da matukar muhimmanci wajen nazari da amincewa da manyan manufofin ilimi da karfafa hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Ya ce:

"Wannan taro wuri ne da ake musayar sababbin ra’ayoyi, tare da gano sababin matsaloli da kuma samar da shawarwari masu kyau domin tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi a jihar."

Gwamnan Kano ya samu lambar yabo

A baya, kun samu labarin cewa gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi zarra a tsakanin gwamnonin da ke jihohin nahiyar Afrika ta fannoni da dama, ciki har da ilimi.

An mika kyautar ga wakilan gwamnan a Casablanca, Moroko, inda aka bayyana ayyukan gwamnatin Kano a fannin shugabanci nagari a matsayin abin koyi a sassan nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Ginin makaranta ya rufta kan ɗalibai suna tsakiyar karatu a Yobe, an rasa rai

A jawabinsa na godaiya, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sadaukar da kyautar ga jama'ar Kano da suka zabe shi, tare kuma da ci gaba da karfafa masa gwiwa wajen aiwatar da ayyukan cigaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel