Bayanai Sun Fito kan Dalilan Shugaba Tinubu na Kin Nada El Rufa'i Minista

Bayanai Sun Fito kan Dalilan Shugaba Tinubu na Kin Nada El Rufa'i Minista

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya ba shugaba Bola Ahmed Tinubu kariya daga zargin da Nasir El–Rufa'i ya yi masa
  • Tsohon gwamnan Kaduna ya ce ba majalisa ce ta ki amincewa da shi a matsayin minista ba, shugaban kasa ne ya sauya ra'ayinsa
  • Sai dai Omokri, ya ce babu kamshin gaskiya a kalaman El–Rufa'i, domin ba shi kadai ne ya samu makamanciyar matsalar a majalisa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaTsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Reno Omokri, ya fadi dalilin da ya sa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bai samu mukamin minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Omokri ya ce El-Rufa’i ya kasa tsallake tantancewar tsaro ba kamar yadda aka yi wa sauran, kuma Majalisar Dattawa ba ta tabbatar da shi ba, sabanin yadda tsohon gwamnan ke ikirari.

Kara karanta wannan

"Mun inganta tsaro," Shugaba Tinubu ya yi magana bayan El Rufai ya faɗi maganganu

Nasir
An bayyana abin da ya hana tsohon gwamnan Kaduna ya zama Minista Hoto: Nasir El–Rufa'i/Reno Omokir/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Omokri ya soki El-Rufa’i kan zarginsa da cewa shugaba Tinubu da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA) ne suka hana shi samun mukamin minista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa majalisa ta ki amincewa da El-Rufa’i?

Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya so nada Nasir El-Rufa’i ta hanyar tura sunansa zuwa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa.

Ya ce:

“Babu abin da ya fi wannan kasancewa ba gaskiya ba. Hakikanin gaskiya shi ne cewa shugaba Bola Tinubu ya zabi Malam Nasir El-Rufa’i a matsayin minista, kuma kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, ya aika sunansa zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa.”

Omokri ya kare Tinubu daga zargin El–Rufa'i

Reno Omokri ya bayyana cewa babu wanda ya kamata Nasir El-Rufa’i ya zarga game da gaza samun mukamin minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sai kansa.

Kara karanta wannan

Muƙamin Minista: Tinubu ya fadi abin da ke damun El-Rufai, ya ba shi shawarwari

Kaduna
Omokri ya ce ba El–Rufa'i kadai aka hana kujerar minista ba Hoto: Nasir El–Rufa'i
Asali: Facebook

Ya ce:

"A yayin tantancewa a Majalisar Dattawa, an bukaci samun tabbacin tsaro daga hukumomin leken asiri na cikin gida da na kasa da kasa, kuma an gano cewa Nasir El-Rufa’i ya gaza tsallake wannan tantancewa gaba ɗaya.
"Saboda wadannan dalilai da wasu karin la’akari, Malam Nasir El-Rufa’i ya kasa samun takardar amincewa ta tsaro, kuma hakan ya sa Majalisar Dattawa ba ta iya tantance shi ba. Shi ne ya kamata ya dora wa laifi, ba Shugaban Kasa ko NSA ba.
"’Yan Najeriya za su tuna cewa ba Nasir El-Rufa’i kadai ne aka ki tantancewa ba. Shi da wasu mutum biyu, ciki har da Danladi Sani daga Jihar Taraba da Stella Okotete daga Jihar Delta, an yi watsi da su domin hukumomin tsaro sun ki amincewa da su."

Shugaba Tinubu ya ba El Rufa'i shawarwari

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta mayar da martani ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, kan korafinsa na rashin samun mukamin minista.

Kara karanta wannan

"Mun raba gari," El-Rufa'i ya fadi abin da ya kashe abotarsa da Uba Sani, Ribadu

A cewar hadimin shugaban kasa a kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, shugaba Tinubu ya ba El-Rufa’i shawara kan korafin da yake yi, amma tsohon gwamnan bai daina gunaguni ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.