'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, Sun Tafka Barna Mai Yawa

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, Sun Tafka Barna Mai Yawa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Ƴan bindigan sun hallaka mutane ciki har da wasu ƙananan yara a hare-haren da suka kai a wasu ƙauyukan ƙananan hukumomin Gusau da Bukkuyum
  • Miyagun sun kuma yi awon gaba da mutane masu yawa a hare-haren waɗanda aka kai a daren ranar Lahadi da safiyar ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun hallaka mutane huɗu ciki har da yara biyu a wasu hare-hare da suka kai a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a hare-haren da suka kai a sassa daban-daban na jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a Katsina, sun hallaka bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hare-haren

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne tsakanin daren ranar Lahadi da safiyar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, 2025.

Ƴan bindigan sun kai waɗannan hare-haren ne a ƙananan hukumomin Gusau da Bukuyyum, inda suka kai farmaki kan jama’a ba tare da wata shakka ba.

A garin Shemori da ke cikin gundumar Mada, ƴan bindiga sun yi garkuwa da mata guda shida da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Lahadi.

Wannan lamari ya jefa jama’ar yankin cikin tsoro da fargaba, kasancewar wannan ba shi ne karon farko da irin hakan ke faruwa ba.

Da sanyin safiyar Litinin, wasu gungun ƴan bindiga sun sake afkawa al’ummar Kairu da ke gundumar Zugu, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance yawansu ba.

Waɗanda suka tsira daga harin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun shiga garin ne da mugayen makamai, suna harbe-harbe tare da tsoratar da jama’a.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga, sun soye.miyagu masu yawa

Ƴan bindiga sun ƙona mutane

Ƴan bindigan sun kuma kai wani hari a Hayin Bajumi da ke cikin garin Mada a ƙaramar hukumar Gusau.

A yayin harin, sun cinna wuta a gidan wani mutumi mai suna Aliyu Usman. Abin takaici, gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar ƴaƴansa biyu, Ishaq Aliyu mai shekaru biyar da Jafar Aliyu mai shekaru biyu.

Bayan haka, maharan ba su tsaya nan ba. Sun kuma yi garkuwa da matar makwabcin Aliyu Usman tare da jaririnta mai shekara guda kafin suka tsere da su zuwa cikin daji.

Mutane na cikin fargaba a Zamfara

Waɗannan jerin hare-haren na ƙara tsananta matsalar tsaro a jihar Zamfara, inda jama’a ke ci gaba da rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas.

Al’umma sun sha yin kira ga hukumomi da su ɗauki matakan gaggawa domin magance wannan matsala da ta addabi yankin.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a Katsina.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙaro rashin imani, sun kashe mutane kusan 20 a garuruwa 2

Ƴan bindigan sun kashe mutanen ne bayan sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka guda biyu na ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng