'Laifin Meye na Yi Muku?' Sheikh Yabo Ya Dura kan Masu Cewa Ya Yi Mummunar Karshe

'Laifin Meye na Yi Muku?' Sheikh Yabo Ya Dura kan Masu Cewa Ya Yi Mummunar Karshe

  • Shahararren malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya caccaki wasu yaran 'yan siyasa da ke jihar Sokoto
  • Malamin ya koka yadda wasu ke cewa wai ya yi mugun ƙarshe ko tsufa ta yi gardama, ya yi musu mummunar addu'a
  • A cikin faifan bidiyo, Sheikh Yabo ya tambaya ta yaya mutum zai yi mugun ƙarshe ba tare da ya mutu ba, ya ce jahilci da hassada ke damunsu
  • Malamin ya zargi cewa wasu yan siyasa kunya ce ta kama su domin ba su tsinana masa komai ba, ya roki Allah ya ƙara musu ciwon hauka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Da alamu wasu yaran siyasa ko iyayen gidansu sun kai Sheikh Bello Aliyu Yabo makura a sakamakon wasu kalamansu.

Shehin malamin ya koka kan yadda yaran wasu yan siyasa ke cewa wai Bello Yabo ya yi mugun karshe ko tsufa ta yi masa gardama.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa a kan sake neman takara a Najeriya

Wasu yan siyasa sun fusata Bello Yabo a Sokoto
Sheikh Bello Yabo ya yi mummunar addu'a ga wasu yaran yan siyasa a Sokoto. Hoto: Sheikh Bello Aliyu Yabo.
Source: Facebook

Bello Yabo ya fusata da kalaman wasu yan siyasa

Sheikh Yabo ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

Shehin malamin ya yi tambaya cewa ta ya mutum zai yi mugun karshe ba tare da ya mutu ya bar duniya ba.

Malamin ya tabbatar da cewa babu abin da ke damunsu sai hassada da mugun jahilci da kuma jin kunya.

"Wasu yaran yan siyasa suna cewa Bello Yabo ya yi mugun karshe, kun ji su? Wai na yi mugun karshe to me na yi? Wane laifi na yi da ke nuna na yi mugun karshe.
"Sannan wanda bai mutu ba ana cewa ya yi mugun karshe, ga ni nan har yanzu, kaddara wasu laifuffuka nake yi, yanzu ina iya tuba ko a'a?
"Idan ba jahilci da hassada ba ta yaya mutun zai ce na yi mugun karshe, wai Bello Yabo ya yi mugun karshe tsufa ta yi gardama.

Kara karanta wannan

'Don Allah ka bar ni': Ribadu ya yi martani ga El-Rufai bayan kalamansa kan zaben 2031

Sheikh Bello Yabo ya fusata da ke yi masa fatan sharri

Source: Facebook

'Hassada ce kawai' - Sheikh Yabo ya magantu

Sheikh Yabo yake cewa kawai kunya ce ta kama su saboda ba su tsinana masa komai ba yayin da wasu sun kai yi mai abin alheri.

Malamin ya kara da cewa:

"Kunya su ke ji suna tare da Bello Yabo ba su yi masa komai ba, wasu sun zo sun ka yi mai, kun san tabarmar kunya da hauka ake nade ta.
"Ina rokon Allah ka da ya kawo musu sauƙin haukar da ta kama su kuma ka da ya shiryar da su, Ubangiji ya sa su ci gaba da haukacewa."

Yabo ya magantu kan alakar Abba da Kwankwaso

Kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan masu neman raba kan jagororin NNPP a Kano.

Malamin ya ce masu neman kawo rigima a tsakanin Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba su kyauta ba ko kadan.

Kara karanta wannan

'Wallahi na kusa mutuwa': Kalaman tsohon sanata kenan makwanni kafin mutuwarsa

Sheikh Yabo ya yi magana ne bayan wasu mutane sun yawaita kiran kalmar 'Abba tsaya da kafarka' a jihar Kano a kwanakin baya.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa,

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.