'Yan Bindiga Sun Kai wa Fulani Makiyaya Hari, An Sace Basarake da Wasu Mutane 38

'Yan Bindiga Sun Kai wa Fulani Makiyaya Hari, An Sace Basarake da Wasu Mutane 38

  • ‘Yan bindiga sun kai farmaki garin Janjala da ke Kagarko, jihar Kaduna, inda suka sace mutane 37, ciki har da Wakilin Fulani na yankin
  • Maharan sun raba kansu gida uku, suna harbi ba kakkautawa, tare da kwashe shanu daga wuraren Fulani makiyaya da ke kusa da kauyen
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da harin amma ba ta bayar da karin bayani ba, yayin da ake ci gaba da neman agajin jami’an tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – ‘Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai farmaki garin Janjala da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addar sun sace Wakilin Fulani na yankin, Alhaji Atah Adamu Wakili, wata mai shayarwa, da wasu mutane 37.

'Yan bindiga sun sace wakilin Fulani da mutane 38 a jihar Kaduna
'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun sace Wakilin Fulani da wasu mutum 38. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Maharan sun kuma kwashe shanu da dama daga garin yayin harin da suka kai da yamma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbi malamin addini, sun sace mutum 6 suna tsaka da yin ibada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindigar suka kai farmakin

Wani jagoran al’umma a yankin, wanda ya tabbatar da lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kauyen da manyan makamai a hannunsu.

Jagoran al'ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu kuma suna sanye da kayan sojoji, inda suka raba kansu gida uku suka afka wa gidaje daban-daban.

Ya ce maharan sun rika harbi ba kakkautawa yayin da suka yi garkuwa da mutane da dama daga yankin da ma wasu Fulani makiyaya da ke kusa.

“Misalin karfe 10:00 na dare ne na samu kiran waya cewa an sace Wakilin Fulani na Janjala tare da matansa, babban dansa Abubakar, da wasu mutane 37,” inji jagoran.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yi ta cin karensu ba babbaka na tsawon kusan sa’o’i biyu ba tare da ko fargabar zuwan jami’an tsaro ba.

Kara karanta wannan

An yi arangama a Niger, dan sanda ya dirkawa jami'ar hukumar NIS bindiga, an tsare wasu

Majiyar ta shaida cewa:

“Har sai zuwa karfe 11:23 na dare ne wani daga cikin mazauna garin ya shaida mani cewa dakarun soji daga Kagarko sun shigo Janjala suna harbi sama.
"Amma kafin isowarsu, tuni ‘yan bindigar sun riga sun tsere da mutanen da suka sace da kuma shanun da suka kwashe."

'Yan bindiga na neman kudin fansa

'Yan bindiga sun farmaki wani kauyen jihar Kaduna, sun sace mutane 39
'Yan bindiga sun nemi N50m da suka sace Wakilin Fulani da wasu mutum 38 a Kaduna. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani dan uwan Wakilin Fulanin da aka sace, mai suna Ahmadu Atah, ya tabbatar da harin, yana mai cewa lamarin ya je fa su cikin fargaba.

“Wannan lamari yana damuna matuka, domin ‘yan bindigar sun shigo gidanmu suka sace mahaifinmu, Wakilin Fulani, tare da matansa da ‘ya’yansa da kuma wasu mazauna yankin.
"Yanzu haka ina Kaduna domin wani taro, amma ina rokon jami’an tsaro su hanzarta daukar mataki domin ceto su."

- Inji Ahmadu.

An rawaito cewa wannan harin na zuwa ne bayan wata guda da wani irin sa ya faru a ranar 11 ga Fabrairu, lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu kauyuka uku.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza artabu da 'yan bindiga

Kauyukan su ne: Mai-Iddo, Gidan Makeri, da Kuchimi, inda suka sace matar wani fasto da wasu mutum 15 tare da kona gidaje da amfanin gona.

A wannan lokacin, maharan sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 tare da babura shida matsayin kudin fansa kafin su sako mutanen da suka sace.

Hukumar ‘yan sanda ya tabbatar da harin

Jami’an ‘yan sanda a yankin sun tabbatar da harin, amma ba su bayar da karin bayani ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai daga kiran waya ba kuma bai amsa sakon tes da aka tura masa kan wannan harin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Fulani sun yi arangama da 'yan banga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla mutane biyu suka mutu yayin da ƴan banga da Fulani makiyaya suka yi arangama a ƙaramar hukumar Bosso, jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Gwamnatin jihar Neja ta shaida cewa mutum bakwai na kwance a Asibitin Beji ana kula da lafiyarsu bayan samun rauni a faɗan da ya auku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.