An Ci Gyaran Farfesa Osinbajo kan Alakar Janar IBB da Shugaba Tinubu

An Ci Gyaran Farfesa Osinbajo kan Alakar Janar IBB da Shugaba Tinubu

  • Hadimin Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce akwai gyara a cikin kalaman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo
  • A yayin taron kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, Osinbajo cikin wasa ya ce IBB sun azabtar da Tinubu
  • Sai dai Onanuga ya na ganin wannan kuskure ne, domin IBB ta na daga cikin wadanda suka zaburar da Tinubu ya tsunduma harkar siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce akwai kuskure a kalaman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

A yayin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida a Abuja, cikin wasa Osinbajo ya ce Tinubu ya zo taya masu azabtar da shi murna.

Kara karanta wannan

"Dole Tinubu ya samu nasara da ƙarfin ikon Allah," Minista ya hango abin da zai faru a 2027

Tinubu
Onanuga ya ci gyaran Osinbajo Hoto: @sadixxy
Asali: Twitter

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Onanuga ya ce Babangida shi ne mutumin da ya ba Tinubu kwarin gwiwar shiga harkar siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce ba daidai ba ne Osinbajo ya kira tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida, a matsayin wanda ya gallaza wa Tinubu a baya.

Hadimin Tinubu ya yi wa Osinbajo gyara

Bayo Onanuga ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ya sha fadin yadda Ibrahim Babangida ya ba shi ƙwarin gwiwar shiga siyasa, don haka Osinbajo ya fassara al’amura ba daidai ba.

Ya ce:

“Ina ganin tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi kuskure. Ina ganin cewa Babangida ba shi ne wanda ya takura wa Shugaba Tinubu ba.
Kada mu manta cewa Shugaba Tinubu ya bayyana a jawabinsa cewa yana kallon Babangida a matsayin wani wanda ya zaburar da shi wajen shiga siyasa.”

Hadimin Tinubu ya yabi IBB

Onanuga ya bayyana cewa matsin lamba da takurawar da Tinubu ya fuskanta sun fara ne a zamanin mulkin Janar Sani Abacha.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankan kauna: Fitaccen basarake ya rasu, Tinubu ya jajantawa al'umma

Tinubu
Onanuga ya ce Tinubu na mutunta IBB Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa a lokacin ne Tinubu da wasu ‘yan siyasa suka yi ƙoƙarin sake kafa majalisar dattawa a Legas.

Onanuga ya ce:

“Lokacin da Babangida ya hau mulki, ya zo da tsarin ‘yan siyasa sababbin jini da makamantan su. Tinubu da wasu da dama, waɗanda tun farko suka kasance a matsayi na kwararru ko masu zaman kansu a harkokin kasuwanci, sun fito don shiga siyasa.
Wannan ne ya ja hankalinsa ya shiga siyasa. Don haka, zuwansa taon kaddamar da littafin, don girmama Babangida.”

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara ya kuma jinjinawa Ibrahim Babangida bisa amincewarsa da cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 1993 duk da cewa an makara.

Tinubu ya fadi wani sirrinsa da IBB

A baya, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yada ya yi karfin hali a lokacin mulkin soja, karkashin jagaorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

A yayin ƙaddamar da littafin tarihin Babangida a Abuja, Shugaba Tinubu ya bayyana yadda ya taɓa fuskantar tsohon shugaban mulkin sojan kan jinkirin rantsar da sababbin Sanatoci a 1992.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.