Abubuwan da Ya Kamata Musulmi Ya Yi domin cin Moriyar Watan Ramadan

Abubuwan da Ya Kamata Musulmi Ya Yi domin cin Moriyar Watan Ramadan

A yayin da ake kasa da mako daya a fara azumin watan Ramadan na shekarar 1446, Sheikh Al-Juzuri ya fadi abubuwan da ya kamata Musulmai su mayar da hankali a kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Al'ummar Musulmi na cigaba da shirye shiryen azumin watan Ramadan yayin da ake kasa da mako daya a fara azumi.

Malamai na cigada da wa'azi da jan hankalin al'umma wajen dagewa da yin ibada domin ribantar kwanakin watan.

Sheikh Al-Juzuri
Sheikh Al-Juzuri ya yi nasiha ga Musulmai a kan Ramadan. Hoto: Muhammad Babayo Aliyu
Asali: Facebook

Wani malamin addini a jihar Gombe, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya bayyana wasu matakai da ya kamata kowane musulmi ya dauka a watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ramadan wata ne mai albarka

Sheikh Al-Juzuri ya bayyanawa Legit cewa watan Ramadan babbar dama ce ta aikata alheri, samun albarka, ibada da yin biyayya ga Allah.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Ya kara da cewa wata ne da ke da girma, wata ne mai daraja, wata ne da ladan ayyukan alheri ke ninkuwa a cikinsa, kuma aikata laifi yana da muni fiye da sauran lokuta.

Saboda falalar watan, malamin ya ce ana buɗe ƙofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin Jahannama, kuma Allah yana karɓar tuba daga masu laifi.

Aljuzuri
Malamin addnin, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri yana gabatar da tafsiri. Hoto: Muhammad Babayo Aliyu
Asali: Facebook

Don haka, ya bukaci mutane su gode wa Allah idan suka riski watan wajen amfani da lokaci ta hanyar cika shi da ibada da nisantar abubuwan da Allah ya haramta.

Yin sauri wajen ayyukan alheri

Sheikh Al-Juzri ya ce ga mai imani na gaske, kowane wata lokaci ne na ibada, kuma duk rayuwarsa tana tafiya ne bisa biyayya ga Allah.

Amma a watan Ramadan, yana samun ƙarin ƙwarin gwiwa wajen aikata alheri, zuciyarsa tana ƙara mai da hankali kan ibada, kuma yana komawa ga Ubangijinsa da ƙwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sakkwato ya waiwayi malaman musulunci, an yi masu tanadin Ramadan

"Yana da kyau mutum ya yi amfani da lokacinsa, bai sani ba ko wannan watan ne na karshe a rayuwarsa. Kowa ya yi amfani da damarsa."

- Sheikh Al-Juzuri

Malmin ya ce kwanaki suna wucewa da sauri. Ramadan na zuwa sai ya wuce, kuma kafin mu ankara, sai ya sake dawowa.

A karkashin haka ya ce:

Saboda haka, ya kamata mu gaggauta aikata ayyukan alheri a wannan watan, mu cika shi da abin da Allah yake so da abin da zai amfanemu a Ranar da za mu hadu da Shi.
Tafsir
Al'ummar Musulmi suna sauraron tafsirin Al-Kur'ani azumin 2024. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Ayyuka na musamman a Ramadan

Sheikh Al-Juzuri ya ce akwai wasu ayyuka da ya kamata mutane su mayar da hankali a kai a watan Ramadan. Daga cikin ayyukan ya ambaci:

1. Karatun Al-Kur'ani

Sheikh Al-Juzuri ya ce a watan Ramadan Allah ya saukar da Al-Kur'ani saboda haka ya kamata kowane Musulmi ya ware lokacin karanta shi a watan.

Kara karanta wannan

Limami: "Abin da ya kamata Musulmai su yi kafin a fara azumin watan Ramadan"

"Duk yadda ka ke da dawainiya, ya kamata a ce kana da lokacin karatun Al-Kur'ani a watan Ramadan domin hakan zai amfane ka."

2. Sallolin dare

A kan yawan salloli, malamin ya ce akwai bukatar mutum ya dage wajen yin sallolin dare da ake yi a Ramadan.

Malamin ya ce:

"Da sallar tarawihi da tahajjud duk sallolin dare ne. Duk wanda mutum ya yi to tamkar ya yi sallar dare ne."
"Ya kamata limamai su yi dubi da wadanda suke ja salla domin kaucewa tsawaita tarawihi da zai jawo korar masu rauni,"

3. Ciyar da al'umma

Malam Al-Juzuri ya ce watan Ramadan wata ne da mutane ke yin azumi, saboda haka ya kamata masu kudi su tausaya wajen ciyar da mutane.

A cewar malamin:

'Ba al'umma abinci ya fi tafiya Umrah lada, musamman ga wanda ya riga ya taba zuwa. Saboda haka a mayar da hankali wajen ciyar da al'umma a watan Ramadan."

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Gwamna ya kawo shirin raba abinci kyauta a Ramadan

Hadisai da yawa sun yi magana a kan falalar ciyar da mai azumi, daga cikinsu shi ne za a ba mutum cikakken lada irin na mai azumin da ya ciyar."

4. Itikafi

Sheikh Al-Juzuri ya bayyana cewa itikafi ibada ce da ake so mai azumi ya yi saboda Annabi (SAW) ya kwadaitar da yin hakan kuma shi ma ya yi.

"Duk wanda ya ke da lokaci da dama yana da kyau ya yi itikafi domin aiki ne mai lada kuma zai ba shi damar yin ibada sosai.
"Kuma ya kamata duk wanda ya shiga ittikafi ya kiyaye dokokinsa domin kaucewa ba ta aikinsa."

5. Umrah

Sheikh Al-Juzuri ya yi kira ga wadanda suke da wadata su ribaci zuwa Umrah a watan Ramadan domin hakan ma ibada ne.

Makka
Al'ummar Musulmi na ibada a Makka. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Sai dai malamin ya ce:

"Ciyar da alumma shi ya fi a kan tafiya Umrah. Akwai wanda zai tafi Umrah a nan Gombe amma a sakamakon wata nasiha da na taba yi sai ya fasa ya ciyar da talakawa da kudin"

Kara karanta wannan

"Allah ne ya jaraba mu," Gwamna ya faɗawa babban malami abin da bai sani ba

"Da mutane sun san falalar ciyar da al'umma da sun rage tafiya Umrah a zumi suna ciyar da bayin Allah"

- Sheikh Al-Juzuri

An kama mai damfara da sunan Izala

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce an kama wani mai damfara da sunan kungiyar.

Sheikh Bala Lau ya ce mutumin ya dade yana cutar mutane da sunan Izala kafin hukumar DSS su kama shi a makon da ya wuce a Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel