Jam'iyyar NNPP Ta Dakatar da Sanata Kawu Sumaila da Wasu Ƴan Majalisa 3
- Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya shaida wa Legit cewa ana zargin Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisa da rashin mutunta shugabanni
- Ya ce wannan, da wasu dalilai ne ya sa aka ɗauki matakin ladabtar da su ta hanyar dakatarwar har sai kwamitin binciken da aka kafa ya zauna
- Ya ce sauran wadanda aka dakatar su ne Alhassan Rurum, Abdullahi Sani Rogo da Aliyu Madakin Gini bayan an gansu suna alaƙa da ƴan adawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP a Kano ta dauki matakan ladabtarwa kan wasu membobinta, ciki har da Sanata da wasu ‘yan majalisa, bisa zargin cin amanar jam’iyya. Shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a Kano a ranar Litinin kwana guda bayan Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya halarci taron Kawu.

Asali: Facebook
Dungurawa ya shaida wa Legit cewa wadanda aka dakatar sun hada da Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu; Alhaji Abdullahi Sani Rogo, mai wakiltar mazabar tarayya ta Rogo.
Sauran wadanda aka dakatar sun hada da Alhaji Alhassan Rurum, mai wakiltar Rano/Kibiya; da Ali Madakin Gini, mai wakiltar mazabar tarayya ta Dala har zuwa bayan ganawa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin NNPP na dakatar da ƴan majalisar
Alhaji Hashimu Dungurawa ya bayyana cewa jam'iyyarsa ce ta yi wa Kawu Sumaila da sauran ƴan majalisar da suka bijire mata komai bayan APC ta yi watsi da su.
Ya ce;
"Na farko dai mun dakatar da su biyo bayan abubuwan da suke yi wanda ko shakka babu ya ta'allaka ga cin mutuncin jam'iyya, da wulakanta shugabanni da yi wa jam'iyya zagon kasa."
Ya bayyana cewa wadanda aka dakatar sun yi watsi da duk wani kira da ake yi na halartar taron jam'iyya.
An zargi Kawu da watsi da jam'iyyar NNPP
Jam'iyya mai mulki a Kano ta bayyana cewa Kawu Sumaila ya rika harka da makiyansa da suka wulakanta shi a baya.

Asali: Facebook
Shugaban jam'iyya na jihar, Hashim Dungurawa ya ce;
"Misali, Mai girma gwamnan jihar Kano, ya yi taro kala-kala wanda yake na ci gaban al'ummar jihar Kano, wanda ya shafi inda suka fito, amma ba mu taɓa ganinsu ba."
"Mai girma jagora, ya sha kiran taro na masu ruwa da tsaki, a bila dake titin Miller ko a Abuja, ba mu taɓa ganinsu ba.
"Hasali ma, kwanan nan mu kayi taro,wanda duk wani zaɓaɓɓe da wanda ke da ruwa da tsaki ya halarci wannan taro, amma abin takaici, wannan mutane guda hudu da na lissafa mi ki, ba su zo ba."
NNPP ta kafa kwamitin binciken yan majalisarta
Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa yanzu haka an kafa kwamitin da zai yi zama na musamman domin binciken zargin cin amanar jam'iyya da ake zargin Kawu Sumaila da takwarorinsa da aikata wa.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar
Hashim Dungurawa ya tabbatar da cewa bayan wannan zama, za a iya yafe wa ƴan majalisar matukar sun nuna nadama, ko kuma a ɗauki matakin da ya wuce wannan.
Manyan APC sun halarci taron ɗan majalisar NNPP
A baya, mun wallafa cewa Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Yunusa Sarina sun aurar da ƴaƴansu ga juna a garin Sumaila na Jihar Kano.
Sai dai manyan ƴan siyasar da suka halarci bikin ɗaurin auren jiga-jigan jam'iyyar APC ne da suka haɗa da Abdullahi Ganduje, Barau Jibrin da Sanata Ahmed Lawan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng