Ramadan: Abubuwa 5 da Ake Fargabar Tsadarsu za Ta Ƙaru da Azumi
Yayin da ya rage kasa da awanni 48 a dauki azumin watan Ramadan, 'yan kasuwa a Kano sun tabbatar da cewa akwai alamun sauki zai tabbata a kan kayan da ake amfani da su wajen buda baki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Lokuta kamar watan Ramadan da sallah sun saba zuwa da hauhawar farashi, musamman na muhimman abubuwa da ake amfani da su, har da mai, dabino, sukari, gero, wake da kankara.
Tun kafin watan ya kama ne aka fara samun saukin tsadar kayan abinci a kasuwannin da ke jihohin Arewa, daga ciki, har da jihar Kano da ta kunshi manyan kasuwanni.

Asali: Getty Images
Legit ta gana da 'yan kasuwa da masu shirin kulla cinikin kankara da watan azumi, kuma sun nanata cewa kar talaka ya ji komai, domin sauki ya samu daga Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin bayanan farashin wasu daga cikin kayan da masu azumi za su yi amfani da su daga masu ruwa da tsaki a wasu kasuwannin Kano.
1. Ramadan: Farashin sukari a Kasuwar Singer
Sukari, yana daya daga cikin abubuwan da ake cinikinsa ainun da azumin watan Ramadan, ganin yadda ya zama ginshikin kunu, shayi da lemukan da ake bude baki da su.
A kowace shekara a kan samu farashinsa ya hau, a wasu lokutan har ya dan yi karanci a shagunan cikin unguwa, sai dai bana, shugabannin kasuwa sun ce ba za a samu haka ba.
A tattaunawarsa da Legit da Kwamred Bashir Madara, jami'in hulda da jama'a na kasuwar Singer ya bayyana cewa mako uku ke nan farashin sukari bai tashi ba.
Ya ce:
"Buhun sukari yanzu N80,000, satin da ya wuce ma haka, sati biyu ma da suka wuce haka farashin yake."
2.Ya farashin gero zai zama da Ramadan?
Alhaji Mustapha Yusuf Mai Kalwa, shugaban kungiyar kasuwar hatsi na kasuwar Dawanau ya shaida wa Legit cewa Allah SWT ya amsa addu'ar bayinSa na samar da sauki.
Ya ce kayan abinci a kasuwar ya sauka matuka, sai dai farashin shinkafa ne har yanzu bai yi saukar da ya zo daidai da na sauran kayan hatsi ba.
Alhaji Mai Kalwa ya ce:
"Gero sati biyu da ya shige, ana sayar da buhunsa tsakanin N58,000 zuwa N57, 000, amma yanzu har N52,000 za ka iya samun gero."
"Sannan wake ana sayar da shi N105,000, 108,000, N110,000, yanzu zaka iya samun na N90,000n N92,000, N95,000 zuwa N100,000.
"Sannan ita masara ana sayar da ita N55,000, yanzu za ka iya samu a kan N52,000 zuwa 50,000 ma za ka iya samu.
Ya bayyana cewa dama a irin wannan lokaci ne ake samun hauhawar farashi, amma sai Allah SWT ya kawo sauki.

Asali: Facebook
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar ya dora alhakin tsadar da ake samu a kan masu sayar da kayayyaki a cikin unguwanni, inda ya bayyana cewa ya kamata su ji tsoron Mahaliccinsu.
3.Farashin kankara ba zai tashi sosai ba
Wani mai sayar da kankara a Kano ya tabbatar wa Legit cewa ganin yadda abubuwa suka yi sauki, ba a sa ran farashin kankara zai haura N500, musamman idan wuta ta na samuwa.
Ya ce a halin yanzu, ana sayar da kankarar ruwan babbar leda a kan N200 a wajensa, kuma yadda gari yake zuwa da lullumi, zai kara taimaka wa wajen dakile tashin farashinta.
Ya ce:
"Yanzu dai kankara ba ta tsada, saboda farashinta ba ya wuce N150 zuwa N200. Sai idan aka yi rashin sa'a rana ta kwalle, za ta tashi har zuwa akalla N400, N350 zuwa N300."
4. Farashin man gyada gabanin Ramadan
Badamasi Ibrahim wani mai sayar da man gyada ne a kasuwar Galadima dake Kano, ya ce a wannan lokacin an samu saukin farashin man ba kamar lokutan baya ba.
Ya ce duk da haka, ana sa ran nan gaba kadan, wato zuwa cikin azumi, farashin zai kara karye wa, wanda ke nufin jama'a za su kara jin sauki.
Ibrahim ya kara da cewa:
"Gaskiya mun samu sauki, shi kan shi farashin man yana dan raguwa. Jarkar mai na lita 25 da ana sayarwa N85,000, amma yanzu da taimakon Allah yana raguwa, yanzu N72,000 ake sayar da shi."
4. Ana sa ran farashin dabino zai daidaita
Ibrahim Hashim, wani mai sayar da dabino ne a jihar Kano, ya bayyana cewa kamar sauran kayayyakin amfanin yau da kullum, su ma sun yi rangwame.
Amma ya ce duk da ba sa fata, akwai yiwuwar farashin ya dan hau kadan, duk da haka yana ganin ba zai kai na shekarun baya ba.
A kalamansa:
"Farashin dabino a yanzu ya yi sauki, ya yi ik rage kudi. Farashinsa ya danganta, kin san shi kilo ake auna shi. Kwanonsa ya danganta, wasu su ce N7,000, wasu N7,500.
"Gwangwanin dabino yanzu ana sayar da shi a kan N500, wasu N450, wasu kuma har N400. Ba yadda ba ta kamawa."
Ramadan: Kayan abinci sun yi sauki
A wani labarin kun ji cewa, rahotanni daga kasuwanni sun tabbatar da yadda farashin kayan abinci da sauran nau'in hatsi yana kara sauki, duk da cewa ana dab da fara azumin Ramadana.
Bincike ya tabbatar da cewa ana samun saukin ne a yawancin jihohin Arewacin Najeriya, inda kayan hatsi kamar su shinkafa, gero, masara, dawa da sauran kayan abinci ke kara yin sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng