An Bankado Umarnin Tinubu da zai Illata Arewa, NARTO Ta Gargadi Gwamnati
- Kungiyar NARTO ta bayyana damuwa bisa sabon umarnin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba da a kan manyan motoci masu dakon fetur
- Shugaban kungiyar na kasa, Yusuf Othman, ya ce sabon umarnin zai zamo barazana ga wadatuwar man fetur zuwa Arewacin Najeriya
- Ya kara da cewa yanzu haka, suna nazari a kan irin illar da sabon matakin zai jawo masu da dabarar da za a yi wajen rage yawan asarar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Kungiyar direbobin manyan motoci (NARTO) ta bayyana damuwa kan tasirin da haramcin da Gwamnatin Tarayya ke shirin kakabawa manyan tankokin dakon mai.
Haka kuma, Kungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya shiga lamarin don rage tasirin da haramcin zai yi wa masu sana’ar.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar

Asali: Facebook
A cewar labarin da ya kebanta ga Jaridar Punch, NARTO ta bayyana cewa haramcin, wanda aka sanar makon da ya gabata, zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ce ta sanar da matakin, bisa la’akari da yawan hadurra da fashewar tankoki masu dakon fiye da lita 60,000 a wasu jihohin kasar.
Umarnin Tinubu zai rage kai fetur Arewa
Shugaban NARTO na kasa, Yusuf Othman, ya ce hana manyan tankoki daukar lita 60,000 zuwa sama zai rage yawan fetur, da ake shigar wa Arewa.
Ya bayyana cewa shiyyar ta dogara ne kacokan ga fetur din da ake jigila daga Kudancin kasar domin amfaninsu na yau da kullum.
Ya kara da cewa:
“Haramcin da zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025, zai hana manyan tankoki fiye da lita 60,000 daga yin lodin mai a matatun man fetur da kuma zirga-zirga a manyan hanyoyin tarayya.
Daga ranar 1 ga Oktoba, 2025, za a kara rage iyakar lodin zuwa lita 45,000 a kowanne tanka.”
NARTO na kara duba umarnin Tinubu
Othman ya ce kungiyar na nazarin wannan sabon tsari tare da tattaunawa da membobinta don kimanta asarar da za ta iya haifar masu da zai kai sama da Naira biliyan 300.

Asali: Facebook
Ya kuma nuna damuwa kan yadda kusan direbobi 2,000 da yaran mota akalla 2,000 da iyalansu za su iya shan wahala sakamakon wannan sabon umarni.
Ya ce:
“Muna duba yiwuwar kera kananan tankoki don dacewa da sabuwar dokar ta gwamnati. Haka kuma, muna nazarin hanyoyin da za mu iya amfani da su wajen cin gajiyar manufofin Gwamnatin Tarayya game da amfani da iskar gas (CNG) da inganta."
“A cikin 'yan kwanaki masu zuwa, za mu fitar da matsaya a hukumance kan lamarin. Amma a halin yanzu, mun karbi umarnin gwamnati da hakuri.”
Gwamnatin Tinubu ta dakatar da jigiliar tankoki
A wani labarin, mun wallafa cewa hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta dauki matakin hana tankokin mai masu daukar fiye da lita 60,000 hawa titunan kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta bayyana daukar matakin ne biyo bayan yawan hadurran da ake fuskanta sakamakon fashewar manyan tankokin mai, wanda ke haddasa asarar rayuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng