Ministan Tsaro Ya Yi Albashir ga Arewa kan Matsalar Ta'addanci, Ya Tabo Alaka da Nijar
- Ministan Tsaro, Alhaji Muhammed Badaru Abubakar, ya magantu kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya
- Badaru ya bayyana cewa an samu ci gaba wurin inganta tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya
- Ya danganta nasarar da kokarin gwamnati ke samu da hadin gwiwar jami'an tsaro a jihohin Zamfara, Sokoto, Niger, Katsina da Kaduna
- Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da ‘yan ta’adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja -Ministan Tsaro, Muhammed Badaru Abubakar, ya ce tsaro ya inganta a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Badaru ya ce wannan ci gaba ya samu ne sakamakon kokarin da ake ci gaba da yi na yaki da ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto, Niger, Katsina da Kaduna.

Kara karanta wannan
2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya

Asali: Facebook
Yaushe gwamnati za ta kawar da ta'addanci?
Ministan ya fadi hakan ne yayin wata hira da manema labarai a karamar hukumar Birnin-Kudu a jihar Jigawa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na kawar da dukkan nau'ikan ta’addanci a kasar nan kafin karshen wannan shekara.
A cewarsa:
"Idan muka kalli ra’ayoyin jama’a, kungiyoyin farar hula da mutanen da abin ya shafa, kowa na cewa an sami ci gaba wurin yaki da ta'addanci."
"Ko da yake ana samun ci gaba, za mu ci gaba da kokari kuma muna ba dakarunmu duk abin da suke bukata domin kawo karshen matsalar tsaro."
Dangane da matsalar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, ministan ya ce kasashen biyu suna da kusanci kamar ‘yan uwan juna, cewar The Nation.

Asali: Facebook
Badaru ya fadi alakar Najeriya da Nijar
Ya ce:
"Mun sha fada cewa mu ‘yan uwa ne, ba za mu taba yin wani abu da zai cutar da Jamhuriyar Nijar ba."
Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wurin bankado ‘yan ta’adda da masu basu goyon baya.
Ya kara da cewa:
"Muna bukatar jama’a su taimaka wa jami’an tsaro da ingantattun bayanai kan inda ‘yan ta’adda da magoya bayansu suke domin kawar da su."
Legit Hausa ta tattauna da wani dan Zamfara
Kwamred Ahmad Muhammad wanda ke Zamfara a yankin Arewa maso Yamma ya ce to wanda bai yankin da ake fama zai iya cewa an samu ingantaccen tsaro.
"Amma gaskiya a yankunan da muke babu wani inganci saboda mafi yawan al'umma suna fuskantar kalubale saboda yan bindigar kamar ba su karewa"
- Ahmad Muhammad
Matashin ya bukaci gwamnati ta kara kaimi saboda ganin an kawo karshen ta'addanci a Najeriya baki daya.
Badaru ya sha alwashin karar da yan bindiga
Kun ji cewa Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya jagoranci kaddamar da sababbin jiragen yaƙi samfurin ATAK-129 a jihar Katsina.
Badaru ya ce jiragen za su taimaka wajen kawo karshen ƴan bindiga da dukkan nau'in miyagun da ke kawo cikas a zaman lafiya.
Ministan kuma jinjinawa dakarun sojoji bisa sadaukarwar da suke yi domin tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Asali: Legit.ng