Dubu Ta Cika: Ƴan Sanda Sun Cafke hatsabibin Barawon da Ya Addabi Jigawa da Sata

Dubu Ta Cika: Ƴan Sanda Sun Cafke hatsabibin Barawon da Ya Addabi Jigawa da Sata

  • Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta kama Alhassan Isa, wanda ake zargi da shahara a satar ababen hawa a Karamar Hukumar Kiyawa
  • Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi bayan dogon bincike, inda ya amsa laifinsa, kuma an gano cewa ya taba zama a gidan yari
  • Rundunar ta shawarci masu motoci da ababen hawa su kula da kadarorinsu, su rufe su da kyau, tare da kai rahoton duk abin da ake zargi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta cafke Alhassan Isa, wanda aka fi sani da Tata, wani barawo da ake zargin ya addabi jihar da sace-sacen mota.

A cewar rundunar, wanda ake zargin mazaunin garin Shuwarin ne a karamar hukumar Kiyawa, kuma an same shi da wata mota kirar Mazda 323 Model F.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sanar da fara daukan 'yan sanda a karon farko a 2025

'Yan sanda sun magantu da aka cafke rikakken barawon motoci a Jigawa
'Yan sanda sun cafke rikakken barawon motoci a jihar Jigawa. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

'Yan sanda sun cafke barawon mota a Jigawa

Rahoton Punch ya nuna cewa wani, Abdurrahman Sadiq, ma’aikacin hukumar bincike kan man gyada ta Najeriya, ya kai rahoton sace masa mota a ofishin ‘yan sanda na Dutse a ranar 21 ga Fabrairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sadiq ya bayyana cewa ya ajiye motarsa a kauyen Aujara, karamar hukumar Jahun, inda ya manta makullinta a ciki. Da ya farka da safiya, sai ya tarar da an sace motar.

Binciken farko ya nuna cewa wasu da ba a san su ba sun dauke motar daga inda aka ajiye ta, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka fara bincike.

Jigawa: Wanda ake zargin ya amsa laifinsa

Jami’an bincike daga ofishin ‘yan sanda na Dutse da sashen binciken manyan laifuffuka na jihar sun gudanar da bincike, wanda ya kai ga kama Alhassan Isa.

A cewar kakakin rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, wanda ake zargin ya amsa laifinsa a yayin bincike, kuma an gano cewa ya taba zama a gidan yari saboda satar babura da kekunan adaidaita sahu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Rundunar 'yan sanda ta aika sako ga mutane bayan kama barawon mota a Jigawa
Rundunar 'yan sanda ta gargadi mazauna Jigawa bayan cafke barawon ababen hawa. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a kotu domin fuskantar hukunci bisa dokar kasa.

'Yan sanda sun gargadi masu ababen hawa

SP Adam ya tabbatar da cewa za a yi adalci a shari’ar, tare da gargadin jama’a su kula da kadarorinsu don kaucewa satar mota.

Haka nan, rundunar ‘yan sandan ta shawarci masu motocin su rika rufe su da kyau tare da guje wa barin abubuwa masu daraja a ciki.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba ko wani abin hawa da suka fahimci na sata ne ga 'yan sanda mafi kusa.

A karshe, ‘yan sandan Jigawa sun tabbatar da kudirinsu na dakile laifuka da kuma tabbatar da tsaro a fadin jihar.

An cafke wani barawo da aka dade ana nema

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Nasarawa ta kama wani mutum da ake zargi da sata a karamar hukumar Karu da ke cikin jihar.

A wata sanarwa da ya fitar a Lafia, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel ya ce wanda ake zargin na cikin jerin mutanen da ake nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.