'Yan Sanda Na Neman Wasu Ma'aurata Ruwa a Jallo, An Saki Hotunansu da Adireshi
- Rundunar ‘yan sanda ta ayyana wani miji da mata a matsayin waɗanda take nema ruwa a jallo bisa zargin aikata sojan gona da zamba
- Waɗanda ake nema su ne Hafsat Kabir Lawal, mai shekara 37, da Baba Sule Sadiq, mai shekara 44, ‘yan asalin Kaduna da Katsina
- Rundunar ta ba da lambobin waya domin a tuntube ta idan an gano su, sannan ta sanya tukuici mai tsoka ga wadanda suka cafke su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ayyana wasu da ake zargin miji da mata ne a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo.
Waɗanda rundunar ke nema ruwa a jallo su ne: Hafsat Kabir Lawal, mai shekaru 37 da Baba Sule Sadiq, mai shekaru 44.

Asali: Twitter
Rundunar 'yan sanda na neman miji da mata
Legit Hausa ta ci karo da sanarwa ta musamman dauke da sunaye da adireshin wadanda ake zargin a shafukan NPF na soshiyal midiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar rundunar 'yan sandan ta nuna cewa ana neman Hafsat Kabir da Baba Sule bisa zargin hadin kai wajen aikata ta'addanci, sojan gona da cin zamba cikin aminci.
A cewar sanarwar sanarwar, rundunar 'yan sandan, reshen birnin tarayya Abuja ce ke son cafke mutanen biyu.
An ba 'yan Najeriya damar cafke ma'auratan
Rundunar 'yan sanda ta roki 'yan Najeriya da su taimaka mata wajen cafke Hafsat Kabir da Baba Sule.
Sanarwar ta ce 'yan kasa na iya cafke wadannan mutane a duk inda suka gamsu, sannan su mika su ga ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko ofishin rundunar na Abuja.
Rundunar 'yan sanda ta bayar da lambobin waya da za a iya tuntubarta idan aka ga 'ma'auratan', 0901 779 2221 da kuma 0811 111 4878.
'Yan sanda sun yi karin bayani kan ma'auratan

Asali: Facebook
Gida mai lamba 6, layin Kamba, Unguwar Dosa, jihar Kaduna da gida mai lamba 2B, layin Ramat B, Unguwar Rimi, Kaduna, su ne adireshin karshe na wadanda ake nema.
Sanarwar 'yan sandan ta ce:
"Idan aka gansu, a cafke su tare da mika su ga ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kuma ofishin kwamishinan 'yan sandan Abuja.
"Lawal da Sadiq Hausa/Fulani ne, kuma 'yan asalin jihar Katsina da Kaduna ne. Rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwa dauke da bayanan wadanda ake nema.
"A sanarwar rundunar, sashen CID, mai lamba 48, an bayyana tukuicin da za a ba wanda ko wadanda suka cafke mutanen, kamar yadda Sufeta Janar ya ba da umarni."
Kalli hotuna da bayanan ma'auratan a nan kasa:
Kano: 'Yan sanda sun kama miji da mata
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wani ma’aurata da suka sace jaririn wani mutum da matarsa ta haifa ‘yan biyu.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa wanda ake zargi sun hada da Abubakar Sadiq da matarsa, Maryam Sadiq.
A cewar DSP Abdullahi Kiyawa, wadda ake zargin, Maryam ta amsa laifin sata, inda ta bayyana cewa mijinta ya dade yana neman ɗa namiji, shi ya sa ta sace jaririn.
Asali: Legit.ng