Ana Tunkarar Azumi, Wani Sanata a Arewa Zai Rabawa 'Yan Mazabarsa Tallafin N500m
- Sanata Lawal Adamu Usman ya ware Naira miliyan 500 domin tallafawa Musulmai a mazabar Kaduna ta Tsakiya a lokacin Ramadan
- Sanatan ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, domin saukaka wahalar da jama’a ke fuskanta a bana
- Ya bayyana cewa taimakon al’umma a wannan lokaci na azumi yana da muhimmanci, tare da fatan kowa zai samu ladan Ramadan daga Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sanata Lawal Adamu Usman, dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya shirya rabawa 'yan mazabarsa tallafin N500m.
Wannan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki daya ke sa ran fara azumin Ramadana a mako mai zuwa.

Asali: Facebook
Sanatan Kaduna zai raba tallafin N500m
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Lawal ya shaida cewa zai raba tallafin ne ga al'ummar Musulmi na mazabarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, dan majalisar dattawan ya sanar da cewa ba iya 'yan mazabarsa ba, har da ma Musulmai daga wasu mazabun, za su ci gajiyar tallafin.
Sanata Lawal Usman, ya ce yana fata wannan tallafin zai ragewa al'ummar Musulmi radadin tsadar rayuwa da kawo masu sauki a lokacin azumin Ramadan.
Sanatan Kaduna ya aika sako ga 'yan kasuwa
Har Ila Yau, dan majalisar dattawan na Kaduna, ya roki 'yan kasuwa da su taimaka su duba yiwuwar rage farashin kayayyakinsu alfarmar Ramadan.
Dan majalisar ya ce akwai bukatar rage farashin kayan abinci ga mutane la'akari da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.
Sanata Lawal Usman ya ce kowa ya san ana cikin matsin rayuwa, don haka fitar da kayan abinci da sayar da su da araha zai jawo rahamar ubangiji da tarin lada.

Asali: Facebook
Abin da Sanata Lawal Usman ya ce

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
Sanatan Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa yayin da watan Ramadan ke karatowa, ya ware Naira miliyan 500 domin tallafawa al'ummar mazabarsa, musamman Musulmai da wasu daga cikin jama’ar da za su yi azumi.
Ya ce wannan tallafi zai taimaka wajen rage wahalhalun da mutane ke fuskanta, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.
A cewarsa:
"A matsayina na wakilin al'ummata, na dauki nauyin samar da tallafi ga mutanen da ke fama da matsin rayuwa, domin rage musu radadin wahalar da ake ciki a wannan lokaci mai muhimmanci."
Sanatan ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wa jama’a ta hanyar rage farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, don saukaka wahalar da ake fuskanta a bana.
A cewarsa, yin haka ba wai kawai taimako ne ga al'umma ba, har ila yau yana da lada mai girma daga Allah.
Ya ce:
"Ina rokon ‘yan kasuwa da su tausaya wa talakawa, su sayar da kaya cikin rangwame, domin rage radadin matsin tattalin arziki. Idan muka nuna jin kai ga juna, muna da yakinin samun lada daga Allah."
Kiran da sanatan ya yi na karshe
A karshe, sanatan ya yi fatan Allah ya ba kowa ikon yin azumi cikin sauki da albarka, yana mai addu'ar samun nasara da dacewa a wannan wata mai alfarma. "Ina yi mana fatan azumi mai cike da albarka. Allah ya karba ibadunmu, amin," in ji shi.
Wannan tallafi da sanatan ya ware na Naira miliyan 500 na daga cikin kokarin sa na tallafa wa jama'a a lokacin da ake bukatar taimako.
Yana daya daga cikin shirin da ke nuni da yadda ‘yan siyasa ke kokarin rage radadin da matsin tattalin arziki ya haifar ga al’umma, musamman a lokacin ibada irin wannan.
An jinjinawa Sanata Lawal
A zantawar Legit Hausa da wani mazaunin mazabar Kaduna ta Tsakiya, Hussaini Baban Nur, ya yaba da wannan yunkuri na Sanata Lawal Usman.
Hussaini Baban Nur ya ce al'umma na cikin wani mawuyacin hali, don haka tallafin kudin zai sa su yi azumin Ramadan cikin walwala da wadatar abinci.
"Ya yi kokari sosai, Allah ya saka mashi da alkairi. Mutane da dama suna wuni ne da zulumin abin da za su yi buda baki da shi, wasu kuma ba su da abincin sahur.
"Idan har wannan tallafin zai iske talakawa, to tabbas zai sanya farin ciki a zuciyar mutane masu yawa. Wallahi ana cikin wani yanayi.
"Fatan mu shi ne ayi adalci wajen rabon kudin nan. Ka da ace za a ba wakilan jam'iyya, ko wakilan al'umam, a raba su kai tsaye kawai ga mutane, shi zai dakile karkatar da kudin."
- A cewar Baban Nur.
Limaman Yarbawa sun fadi ranar fara azumi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Limamai da Alfa a yankin Yarbawa, Edo da Delta ta bayyana ranar da za a fara azumin Ramadan na 2025.
Sanarwar daga ofishin Babban Mufti na Yarbawa ta tabbatar da cewa azumi zai fara ne a ranar Asabar, 1 ga Maris, 2025.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan sanarwa na daga cikin al’adarta na shekaru da dama, bayan gudanar da jerin taruka da shugabanninta.
Asali: Legit.ng